logo

HAUSA

Jakadan Sin a Kongo(Kinshasa): Shigar Kongo(Kinshasa) shawarar ziri daya da hanya daya na da babbar ma’ana

2021-01-12 11:16:07 CRI

Kasar Kongo(Kinshasa), zango na biyu ne da mamban majalisar gudanarwar kasar Sin kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi ke kaiwa ziyarar a nahiyar Afirka.

Yayin ziyarar tasa, mista Wang Yi ya gana da shugaban kasar da kuma takwaransa na kasar daya bayan daya, kana kasashen biyu wato Sin da Kongo(Kinshasa), sun daddale takardar fahimtar juna kan hadin gwiwar dake tsakaninsu bisa shawarar ziri daya da hanya daya.

Jakadan kasar Sin dake kasar Zhu Jing ya bayyana yayin da yake zantawa da wakilinmu na babban gidan rediyo da talibijin kasar Sin wato CMG a takaice cewa, ziyarar Wang Yi a kasar ta Kong(Kinshasa), ta samu babban sakamako, musamman wajen kara karfafa hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka bisa shawarar ziri daya da hanya daya, da kuma gina kyakkyawar makomar bil Adama ta bai daya ta Sin da Afirka.

Jakadan Sin a Kongo(Kinshasa): Shigar Kongo(Kinshasa) shawarar ziri daya da hanya daya na da babbar ma’ana_fororder_1.JPG

Jakadan kasar Sin dake wakilci a kasar Kongo(Kinshasa) Zhu Jing ya bayyana cewa, “Ziyarar da mamban majalisar gudanarwar kasar Sin, kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi ya yi a kasar Kongo (Kinshasa) ta samu babban sakamako, inda kasashen biyu suka tabbatar da muradun ci gaban huldarsu a nan gaba, kafin wannan, ya taba kai wa kasar ziyara a shekarar 2015, ya kasance zumuncin gargajiya tsakanin kasashen biyu, kuma huldar dake tsakaninsu tana gudana lami lafiya tun daga shekarar 1972. Kawo yanzu wato bayan kokarin da suka yi a cikin shekaru kusan 50 da suka gabata, sassan biyu sun samu babban sakamakon yayin da suke gudanar da hadin gwiwar dake tsakaninsu. Alal misali, a cikin birnin Kinshasa, an ga manyan gine-ginen da kasashen biyu suka gina cikin hadin gwiwa, kamar su fadar jama’a, da filin wasan motsa jiki, da cibiyar fasahar al’adun tsakiyar Afirka da ake ginawa.

A bangarorin cinikayya da zuba jari kuwa, sassan biyu suna gudanar da hadin gwiwa yadda ya kamata, gaba daya adadin jarin da kasar Sin ta zuba a Kongo(Kinshasa) ya riga ya zarce dalar Amurka biliyan 10, kana adadin cinikayyar dake tsakanin kasashen biyu zai kai dala biliyan 7. Ban da haka, abun farin ciki shi ne, bisa takardar fahimtar juna da gwamnatocin kasashen biyu suka daddale yayin ziyarar Wang Yi, Kong(Kinshasa) ta kasance kasa ta 45 dake nahiyar Afirka, wadda ta shiga shawarar ziri daya da hanya daya, lamarin dake da babbar ma’ana, wanda kuma zai taka rawar gani a fannin hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka bisa shawarar, kana zai taka babbar rawa yayin da sassan biyu suke gina kyakkyawar makoma ta bai daya ta Sin da Afirka.”

Jakadan Sin a Kongo(Kinshasa): Shigar Kongo(Kinshasa) shawarar ziri daya da hanya daya na da babbar ma’ana_fororder_2

A cikin shekarar 2019 da ta gabata, kasashen biyu wato Sin da Kong(Kinshasa) sun hada kai domin dakile annobar cutar numfashi ta COVID-19, jakada Zhu Jing yana mai cewa, “Cikin dogon lokaci, kasar Sin da kasar Kongo(Kinshasa) suna gudanar da hadin gwiwa a bangaren kiwon lafiya, saboda Kong(Kinshasa) tana fama da cututtuka masu yaduwa iri daban daban, kuma gwamnatin kasar tana maida hankali matuka kan aikin magance cututtuka masu yaduwa, da kiwon lafiyar al’ummun kasar.

Tun farkon barkewar cutar numfashi ta COVID-19 a kasar Sin, nan take gwamnatin Kongo(Kinshasa) da bangarori daban daban na kasar, sun samar da goyon baya ga kasar Sin ta hanyoyi daban daban, daga baya wato tun daga watan Maris na bara, an samu bullar annobar a kasar ta Kongo(Kinshasa), inda gwamnatin kasar ta dauki matakan kandagarkin cutar ba tare da bata lokaci, amma tana fama da matsaloli da dama. Alal misali, karancin kayayyakin kandagarkin cutar, da kuma karancin fasahohin shawo kan cutar, a daidai wannan lokaci, kasar Sin ta samar da kayayyakin kiwon lafiya ga kasar kafin sauran kasashe, har ta kasance kasa ta farko wadda ta mika kayayyakin kiwon lafiya, tare kuma da aikewa da tawagar kwararrun kiwon lafiya ga kasar, inda kwararrun kasar Sin suka yi wa ma’aikatan kiwon lafiyar kasar horo har sau sama 30, a cikin kwanaki 20 yayin da suke aiki a kasar.”

Game da makomar hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu, jakada Zhu Jing ya bayyana cewa, ana sa ran sassan biyu za su kara karfafa hadin gwiwarsu a bangarorin hakar ma’adinai, da gina manyan kayayyakin more rayuwar jama’a, da tattalin arzikin zamani, da aikin gona da sauransu, yana mai cewa,“A cikin ‘yan shekarun baya bayan nan, sassan biyu sun fi maida hankali kan hadin gwiwar dake tsakaninsu a bangarorin hakar ma’adinai, da gina manyan kayayyakin more rayuwar jama’a. Yanzu haka kasar Kongo(Kinshasa) ta shiga shawarar ziri daya da hanya daya, lamarin da zai samar da sabon kuzari ga hadin gwiwarsu a bangaren gina manyan kayayyakin more rayuwar jama’a. Kana sassan biyu za su kara karfafa hadin gwiwa wajen raya tattalin arzikin zamani, duba da yadda gwamnatin Kongo(Kinshasa) ke kara ba da muhimmanci kan aikin, kuma kamfanonin kasar Sin suna da fasahohi da hidimomi mafiya inganci a duniya. Haka zalika, kasar Sin babbar kasa ce a fannin aikin gona, wadda ke son samar da tallafi ga Kongo(Kinshasa), domin ciyar da aikin gona gaba yadda ya kamata a kasar.”(Jamila)