logo

HAUSA

Kasar Sin ta tinkari kalubaloli iri iri da su faru ba zato a shekarar 2020 kamar yadda ake fata

2020-12-30 09:00:00 CRI

A shekarar 2020 mai shirin karewa, kamar kowace shekara, abubuwa sun faru, kama daga na ban-al'ajabi, da na mamaki, ko tausayi, bajinta, da sauransu. Baya ga irin wadannan abubuwan da muka ambata da farko wadanda kan faru a cikin kowace shekara, a kan kuma kulla dangantaka ko kai ziyarar sada zumunci tsakanin manyan jami’ai da shugabannin kasashe da nufin karfafa dankon zumunci ko huldar cinikayya, ko al'adu, ko tattalin arziki ko ci gaban kimiya da dai sauransu.

Kasar Sin ta tinkari kalubaloli iri iri da su faru ba zato a shekarar 2020 kamar yadda ake fata_fororder_201230-Muhimman abubuwan da suka faru a shekarar 2020-hoto1

Misali, Kasar Sin ta yi nasarar harba na’urar binciken duniyar Chang’e-5, har ma ya dawo wasu samfura, wadanda kasar Sin ta ce za ta raba tare da sauran kasashen duniya, don kara fahimta da ma inganta binciken duniyar wata.

Kasar Sin ta tinkari kalubaloli iri iri da su faru ba zato a shekarar 2020 kamar yadda ake fata_fororder_201230-Muhimman abubuwan da suka faru a shekarar 2020-hoto2

A wannan shekarar ce kuma, kasar Sin ta fara amfani da filin tashi da saukar jiragen saman kasa da kasa na zamani na Beijing-Daixing. A wannan lokacin har ila, kasar ta kera jirgin ruwa dake nutsu a teku mai suna Fendouzhe, wato mai himma da kwazo, jirgin dake iya nutsun zurfin mita 10,909 a teku, da ma sauran nasarori a fannoni daban-daban

Muna fatan samun zaman lafiya, kwanciyar hankali, alheri da karuwar arziki da wadata a duniya baki daya a sabuwar shekara ta 2021. Amin. ( Saminu, Ibrahim/Sanusi Chen)