logo

HAUSA

Mummunar dokar da Amurka ta zartas kan yankin Taiwan ba za ta yi tasiri ba

2020-12-30 20:08:26 CRI

Mummunar dokar da Amurka ta zartas kan yankin Taiwan ba za ta yi tasiri ba_fororder_A

Kwanan nan ne shugaban Amurka ya sanya hannu kan wani shirin dokar kasafin kudi na shekara ta 2021, wanda ya kunshi wata ayar doka kan yankin Taiwan na kasar Sin, sashen ayar dokar, ya nuna cewa, gwamnatin Amurka za ta rika sayar da makamai ga Taiwan, da barazanar mara mata baya wajen shiga muhimman kungiyoyin kasa da kasa da dama. Irin wannan aika-aikar da Amurka ta yi, tsoma baki ne cikin harkokin gidan kasar Sin, da lahanta moriyar kasar, kuma kasar tana nuna adawa da ma yin Allah wadai da shi matuka.

Mummunar dokar da Amurka ta zartas kan yankin Taiwan ba za ta yi tasiri ba_fororder_B

Batun Taiwan, batu ne da ya shafi ikon mallaka gami da cikakken yankin kasar Sin, kana batu ne mai muhimmanci dake jawo hankali a huldar Sin da Amurka. Sanarwa kan kulla huldar jakadanci tsakanin Sin da Amurka wadda aka fitar a shekara ta 1978, ta yi nuni da cewa, Amurka ta amince cewa, gwamnatin Jamhuriyar Jama’ar kasar Sin halaltacciyar gwamnati ce daya tak a kasar. Kuma ‘yan siyasar Amurka sun san da wannan batu sosai.

A halin yanzu, dangantakar Sin da Amurka na cikin wani yanayi mai sarkakiya, tun bayan kulla dangantakar diflomasiyya tsakaninsu. In har sabuwar gwamnatin Amurka dake shirin kama aiki tana son kare muradunta a yankin Asiya da tekun Pasifik, ya zama dole ta kara fahimtar sarkakiyar da hadarin dake cikin batun Taiwan tare da yin hattara, domin kar ta kara tafka kurakurai ko kuma aikata abubuwa masu hatsari.(Murtala Zhang)