logo

HAUSA

Yawan wadanda suka kamu da COVID-19 a Afrika ya zarce miliyan 2.15

2020-11-30 11:11:34 CRI

Cibiyar kandagarki da dakile yaduwar cututtuka ta Afrika wato Africa CDC, ta ce adadin wadanda aka tabbatar sun kamu da COVID-19 a nahiyar Afrika, ya kai 2,150,439.

Wata sanarwa da cibiyar ta fitar, ta ce zuwa jiya Lahadi, yawan wadanda cutar ta yi sanadin mutuwarsu ya kai 51,481.

Sannan, jimilar mutane 1,815,839 da suka kamu da cutar a fadin nahiyar, sun riga sun warke.

Ta ce kasashen nahiyar da cutar ta fi kamari, bisa la’akari da yawan wadanda suka kamu da ita, sun hada da Afrika ta kudu da Morocco da Masar da Habasha .

Yankin kudancin Afrika ne cutar ta fi shafa, duba da yawan adadin wadanda suka mutu da wadanda suka kamu da ita. (Fa’iza Mustapha)