logo

HAUSA

EU da Birtaniya sun shiga makon karshe na cimma yarjejeniya

2020-11-30 10:55:02 CRI

Sakataren harkokin wajen Birtaniya, Dominic Raab, ya ce tattaunawa tsakanin Tarayyar Turai da Birtaniya, dangane da cinikayya bayan Birtaniya ta fice daga tarayyar, ta shiga mako na karshe na cimma cikakkiyar yarjejeniya.

Da yake kira ga EU ta amince da ka’idar da ta shafi kamun kifi, daya daga cikin muhimman bangarorin tattaunawar, akwai alamu Sakataren bai amince da matsayar da EU ta dauka kan batun ba, wadda ke neman yawan kifin da jiragenta ke kamawa a ruwan Birtaniya ya dawo tsakanin kaso 15 zuwa 18.

Dangane da sauran batutuwan da ba a cimma matsaya kansu ba, Dominic Raab ya ce yana ganin ana samun ci gaba dangane da matsayar da Birtaniya ta dauka na cimma yarjejeniyar da bangarorin biyu za su amince da shi, wadda ta shafi jerin ka’idojin cinikayya bayan ficewar Birtaniyar daga kungiyar.

Birtaniya da EU sun dawo da tattaunawa gaba da gaba a ranar Asabar a birnin London, dangane da yarjejeniyar, bayan a watan da ya gabata, wani wakilin EU ya kamu da cutar COVID-19. (Fa’iza Mustapha)