logo

HAUSA

Li Keqiang ya halarci taron firaministocin SCO

2020-11-30 20:26:27 CRI

A yau ne, firaministan kasar Sin Li Keqiang ya halarci taron majalisar firaministocin kasashe mambobin kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai (SCO) karo na 19 ta kafar bidiyo, tare da gabatar da shawarwari kan yadda za a raya kungiyar a nan gaba.

Li ya jaddada cewa, kasarsa tana goyon bayan manufar bude kofa da samun moriya tare, ta kuma himmatu wajen neman hanyar raya kanta yayin da take raba damammaki da sauran kasashen duniya da samar da kyakkyawar makoma ta bai daya ga kungiyar SCO. (Ibrahim Yaya)