logo

HAUSA

Sautin kasar Sin da ke cikin sararin samaniya

2020-11-30 14:51:13 CRI

Na’urar binciken duniyar wata da ake kira Chang’e-5 yanzu haka ta kama hanyar kewayen duniyar wata, kuma abin lura shi ne, na’urar tana dauke da wata waka mai taken “ Believe That Love Will Win” wadda take fitarwa ta sauti da kuma hoton bidiyo, wakar da ke bayyana yadda ‘yan Adam ke kokarin yaki da annobar Covid-19.

Tuni,shekaru 50 da suka wuce, kasar Sin ta isar da sautinta sararin samaniya. A ranar 24 ga watan Afrilun shekarar 1970, kasar Sin ta cimma nasarar harba tauraron dan Adam na farko da ta kera, wanda aka yi masa lakabin Dongfanghong-1 har zuwa sararin samaniya, tauraron da kuma ya dauki wata waka mai taken “The East is Red” har zuwa sararin samaniya, matakin da ya alamanta yadda kasar Sin ta fara shiga zamanin binciken sararin samaniya.

Sautin kasar Sin da ke cikin sararin samaniya

A cikin shekaru 50 da suka wuce, taurarin dan Adam da kuma kumbunan da kasar Sin ta harba zuwa sararin samaniya sun shaida ci gaban da kasar ta samu ta fannin harkokin nazarin sararin samaniya, wadanda kuma suka isar da karin sautin kasar zuwa sararin samaniya.

Ya zuwa shekarar 2007, tauraron dan Adam na farko da kasar Sin ta kirkiro don binciken duniyar wata wanda ake kira Chang’e-1 ya tashi zuwa sararin samaniya tare da jerin kide-kide sama da 30 da aka yi da kayan kidan gargajiya na kasar.  Bayan da ya kama hanyar kewayen duniyar wata, tauraron ya fara fitar da sautin wadannan kide-kiden da al’ummar Sinawa suka zaba a sararin samaniya da ke da nisan kilomita dubu 380 daga duniyarmu.

Sautin kasar Sin da ke cikin sararin samaniya

Sai kuma a shekarar 2008, kumbon Shenzhou-7 mai dauke da ‘yan sama jannati ya isar da wata waka ta daban zuwa sararin samaniya, wakar da shahararren mawakin kasar Sin Zhou Jielun ya tsara tare kuma da rerawa domin wasannin Olympics da aka gudanar a birnin Beijing na kasar Sin.

Sautin kasar Sin da ke cikin sararin samaniya

A hakika, baya ga nazarin kimiyya, an kuma yi kokarin isar da sauti zuwa sararin samaniya ne domin ilmantar da al’umma a kan harkokin sararin samaniya. A ranar 6 ga wata, da misalin karfe 11 da minti 19, kasar Sin ta harba wani tauraron dan Adam da aka lakabta masa sunan tauraron ilmantarwa na Taiyuan, a cibiyar harba taurarin dan Adam na Taiyuan, tauraron da ya dauki wata na’urar da aka adana sautin yara, ciki har da wakoki da kalaman da yara suka yi, kuma yara suna iya sauraron sautinsu da tauraron ya nuna a sararin samaniya bisa na’urar da aka kafa a doron kasa.

Sautin kasar Sin da ke cikin sararin samaniya

Wani daga cikinsu ya bayyana cewa,“Ni kaina ina sha’awar harkokin sararin samaniya sosai, kuma bayan mun shiga wannan harkar sauraron sautinmu a doron kasa daga sararin samaniya, na karfafa niyyata ta yin kokarin ba da gudummawata ga ci gaban harkokin binciken sararin samaniya a kasarmu.”

Ban da haka, an kuma isar da sauti zuwa sararin samaniya ne domin binciken wayin kan da ka iya kasancewa a sauran duniyoyi. A ranar 5 ga watan Satumban shekarar 1977, kasar Amurka ta harba na’urar bincike mai lakabin Voyager-1 a sansanin sojin saman kasar na CCAFS zuwa sararin samaniya, na’urar da ta dauki wani faifan da ya adana gaishe-gaishen ‘yan Adam cikin harsuna 55, ciki har da yarukan kasar Sin.

Sautin kasar Sin da ke cikin sararin samaniya

Malam Yang Yuguang, mataimakin shugaban kwamitin kula da sufurin sararin samaniya na kungiyar kasa da kasa ta binciken sararin samaniya(IAF), wanda kuma shi ne manazarci a cibiyar nazari ta biyu karkashin rukunin nazarin kimiyya da masana’antun binciken sararin samaniya na kasar Sin,  ya bayyana cewa, an tsara faifan da na’urar bincike ta Voyager-1 ta dauka ta hanyar musamman, ta yadda zai iya adana abin da aka saka a ciki cikin wani dogon lokaci a sararin samaniya. Duk da cewa akwai rashin tabbas wajen bin wannan hanyar binciken kasancewar wayin kai a sauran duniyoyi, amma ya shaida yadda ‘yan Adan ke kokarin binciken duniyoyin da ba su sani ba.

Sautin kasar Sin da ke cikin sararin samaniya

Yana mai cewa,“An adana sauti a faifan, ta yadda wata rana idan halittu masu basira da ke rayuwa a sauran duniyoyin da ke da matukar nisa da mu suka samu na’urar, za su saurari gaishe-gaishen ‘yan Adam, wato mun isar da sakonmu gare su.” (Lubabatu)