logo

HAUSA

Adadin manoman da aka kashe a arewa maso gabashin Nijeriya ya kai 110

2020-11-30 10:46:06 CRI

MDD ta ce adadin manoman da aka kashe yayin wani hari da aka kai kauyansu dake jihar Bornon Nijeriya, ya kai 110, yayin da wasu da dama suka jikkata.

Edward Kallon, babban jami’in majalisar mai kula da ayyukan jin kai a Nijeriya, ya yi tir da harin da ake zargin kungiyar BH da kai wa, inda kuma suka sace mata da dama.

Da farko, hukumomi a kasar sun tabbatar a jiya cewa, harin kungiyar BH a kauyen Koshebe na yankin karamar hukumar Mafa, ya yi sanadin kisan manoma sama da 40 yayin da suke aikin a gonakinsu.

Wani ganau ya shaida cewa, lamarin ya auku ne bayan wasu manoma dake girbi, sun kama wani dan BH da ya je wajensu ya na neman abinci.

Cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Asabar, Shugaban kasar Muhammadu Buhari, ya yi Allah wadai da harin, wanda ya bayyana a matsayin na rashin hankali.

Ya ce gwamnati na ba dakaru dukkan taimakon da suke bukata domin daukan matakan da suka dace na kare al’ummar kasar da yankunanta. (Fa’iza Mustapha)