logo

HAUSA

Kasashe da dama sun yi kira da a cire matakan da aka sanya babu gaira babu dalili

2020-11-30 20:45:46 CRI

Kasar Sin ta bukaci kasashen da abin ya shafa, da su kasance masu adalci a harkokin kasa da kasa, su gaggauta soke matakan da suka saba doka da cin zali da suka sanya, su kuma yi aiki da ragowar kasa da kasa wajen hada kai don yakar annobar COVID-19, tare da magance matsalolin da duniya ke fuskanta a halin yanzu.

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, Hua Chunying ce ta bayyana hakan Litinin din nan yayin taron manema labaran da aka saba shiryawa.

A ranar 25 ga wata ne, zaunanniyar tawagar kasar Sin, da Rasha da Afirka ta kudu da sauran kasashe suka shirya taron kwamitin sulhu cikin hadin gwiwa kan batun "Gaggauta kawo karshen matakan da babu gaira ba dalili da aka sanya”. Taron da ya gudana a birnin New York na Amurka dai ya samu halartar wakilai daga sama da kasashe 70 na duniya. (Ibrahim Yaya)