logo

HAUSA

Cutar COVID-19 ba ta hana bude kofa ga kasashen waje a kasuwar hada-hadar kudi ta Sin ba

2020-11-30 14:00:11 CRI

Mataimakin shugaban bankin jama’ar kasar Sin Liu Guiping ya bayyana a gun wani taron shekara-shekara na hada-hadar kudi da aka gudanar a kwanakin baya cewa, ya kamata a kara bude kofa ga kasashen waje don sa kaimi ga kafa sabon tsarin samun bunkasuwa, inda ya ce cutar COVID-19 ba ta hana bude kofa ga kasashen waje a kasuwar hada-hadar kudi ta Sin ba.

Liu Guiping ya bayyana cewa, a mataki na gaba, bankin jama’ar kasar Sin zai ci gaba da sa kaimi ga bude kofa ga kasashen waje a sha’anin hada-hadar kudi. Za a yi kokarin inganta tsarin hada-hadar kudi da kara bude kofa a wannan fanni don kara samar da hidimar ga bangarori daban daban dake kasuwar cikin gida da waje.  Ya kara da cewa, za a yi kokarin bude kofa a kasuwar hada-hadar kudi da hadin gwiwa kan ayyukan more rayuwa don kara samar da sauki ga masu zuba jari dake kasashen waje, ta yadda za su yi amfani da kudin Sin RMB wajen sayen takardun bashi da hannayen jari. Ban da wannan kuma, za a yi kokarin inganta tsarin kudin RMB a kasa da kasa. (Zainab)