logo

HAUSA

Tauraron Change’e-5 na kasar Sin ya sake rage saurin tafiyarsa

2020-11-30 12:46:51 CRI

Tauraron Change’e-5 na kasar Sin ya sake rage saurin tafiyarsa

Hukumar kula da sararin samaniya ta kasar Sin CNSA, ta ce tauraron dan Adam mai bincike na Chang’e-5 na kasar, ya tsaya a karo na biyu da misalin karfe 20:23 na dare a jiya Lahadi.

Hukumar CNSA, ta ce bayan ‘yar tsayuwar, tauraron ya kara tashi a kusa da zagayayyar hanyar dake kewaye da wata.

A mataki na gaba, na’urar dake sauke tauraron zai rabu da wadda ke sanya tauraron tashi da shawagi, inda za ta sauka a hankali a duniyar wata tare da tattaro samfura na farko na kasar daga wajen duniyar dan Adam.

Tauraron ya tsaya ne a karon farko tare da shiga hanyar duniyar wata a ranar Asabar. (Fa’iza Mustapha)