logo

HAUSA

Kafar yada labarai ta Spaniya: Kamata ya yi kasashen yamma su koyi tsarin kawar da talauci daga kasar Sin

2020-11-30 13:48:52 CRI

Tashar yanar gizo ta kasar Spaniya, mai binciken harkokin kasar Sin, ya wallafa wani rahoto mai taken “Kasar Sin wadda ta kawar da matukar talauci a duk fadin kasar” a jiya Lahadi, wanda shahararren mai nazarin harkokin kasar Sin na kasar Xulio Rios ya rubuta.

A cikin bayaninsa, Xulio Rios ya nuna cewa, dukkanin gundumomin dake fama da talauci a kasar Sin sun fita daga kangin talauci, abin da ya bayyana babbar nasarar da kasar ta samu, ya kuma kara gibin dake tsakanin kasarmu da Sin. A cewarsa, dalilin da ya kawo wannan bambanci ya dogaro da tsare-tsaren da kasar ke aiwatarwa. A ganinsa, Sin ta kai ga samun irin wannan gaggarumar nasara ce, saboda kwararan matakan da gwamnati ta dauka a maimakon ta bar kasuwa ta yi halinta。

Xulio Rios ya ce, kamata ya yi kasar Spaniya ta koyi tsarin kawar da talauci da samun ci gaba  daga kasar Sin, kana a kara tumtubar juna tsakanin kasar Sin da kasashen yamma, ta yadda kasashen duniya za su taimakawa juna a wannan fanni. (Amina Xu)