logo

HAUSA

MDD ta yi tir da kisan da aka yi wa manoma shinkafa a Nijeriya

2020-11-30 15:07:32 CRI

Sakatare Janar na MDD Antonio Guterre, ya yi Allah wadai da mummunan kisan da aka yi wa manoma shinkafa da ake zargin ‘yan kungiyar BH da aikatawa a jihar Borno dake arewa maso gabashin NIjeriya.

Cikin wata sanarwa da kakakinsa Stephane Dujarric ya fitar, Sakatare Janar din ya yi kakkausar suka kan harin da aka kai wa manoman a kauyen Koshobe dake kusa da Maiduguri, babban birnin jihar Borno a ranar 28 ga wata, inda aka kashe mutane da dama yayin da wasu suka jikkata ko aka sace su, ciki har da mata.

Sanarwar ta ce Sakatare Janar din ya jaddada kudurin majalisar na taimakawa gwamnatin Nijeriya a yakin da take da ta’addanci da tsattsauran ra’ayi. (Fa’iza Mustapha)