logo

HAUSA

Rika motsa jiki yana taimaka wajen rage barazanar kamuwa da ciwon sukari mai nau’in 2

2020-11-29 18:47:13 CRI

Jami’ar kwalejin London na kasar Birtaniya wato UCL a takaice ta kaddamar da wani sakamakon nazari a kwanakin baya, inda a cewarta, idan ana motsa jiki a ko wace rana, to, za a rage barazanar kamuwa da ciwon sukari mai nau’in 2 kwarai da gaske.

Masu nazari daga jami’ar kwalejin London da jami’ar Cambridge sun gabatar da rahoton nazarinsu cikin mujallar ilmin ciwon sukari ta kasar Jamus, inda suka nuna cewa, sun samu sakamakon ne bayan sun tantance bayanan nazarce-nazarce guda 23 masu ruwa da tsaki da aka gudanar kan mutane fiye da miliyan 1 a kasashen Amurka, Australia, Asiya da Turai.

Da ma ma’aikatar kiwon lafiya ta kasar Birtaniya ta ba da shawarar cewa, ya fi kyau a motsa jiki mai matsakaicin karfi ko kuma mai karfi na tsawon mintoci 150 a ko wane mako, alal misali, yin tafiya cikin sauri, hawan keke da dai makamantansu.

Masu nazarin sun gano cewa, idan an bi wannan shawara, to, za a rage barazanar kamuwa da ciwon sukari mai nau’in 2 da kashi 26 cikin kashi 100. Bayan haka kuma, idan wani ko wata ta motsa jiki da matsakaicin karfi ko kuma da karfi sosai na tsawon awa guda a ko wace rana, to, barazanar kamuwa da ciwon sukari mai nau’in 2 da yake ko take fuskanta za ta ragu da kashi 40 cikin kashi 100.

Masu nazarin sun nuna cewa, sakamakon nazarinsu ya karfafa gwiwar karin mutane su motsa jiki, ta yadda watakila za a rage saurin karuwar yawan masu fama da ciwon sukari mai nau’in 2 a duk duniya.

Duk da haka wasu likitoci sun ba da shawarar cewa, ko da yake motsa jiki ta hanyar kimiyya yana taimaka wa masu fama da ciwon sukari su tabbatar da daidaiton yawan sukari a jini, amma ya zama tilas masu fama da ciwon su shirya ruwan sha, abinci, na’urar binciken yawan sukari da ke cikin jini, da katin tarihinsu kafin su fara motsa jiki, su kuma tsara shirin motsa jiki tare da likita idan suna motsa jiki a lokacin zafi. Kana kuma tsawon lokacin motsa jiki bai kamata ya wuce minti 30 ba a ko wane karo. Ya fi kyau masu fama da ciwon su yi gumi kadan, kada su yi gumi da yawa. Kana kuma kada su yi wanka ko shan abu mai sanyi, da zarar sun kammala motsa jiki.

Tasallah Yuan