logo

HAUSA

Iran ta yi Allah wadai da kashe babban masanin nukiliyarta yayin da kasa da kasa ke nuna damuwa kan lamarin

2020-11-29 16:17:08 CRI

Iran ta yi Allah wadai da kashe babban masanin nukiliyarta yayin da kasa da kasa ke nuna damuwa kan lamarin

Bayan kashe wani babban masanin kimiyyar nukiliyar kasarta, Iran ta yi Allah wadai da kashe jami’in, kana ta yi alwashin daukar fansa, yayin da kasashen dake shiyyar da manyan shugabannin duniya ke bayyana damuwa game da fargabar da ake fuskanta na karuwar tashin hankali a shiyyar tare da bayyana bukatar gaggauta daukar matakan daidaita al’amurra.

Kamfanin dillancin labaran Iran IRNA, ya rawaito shugaban kasar Iran Hassan Rouhani yana cewa, kasar Iran ba za ta taba lamintar wannan mummunan al’amari ya tashi a banza ba. Ya kara da cewa, kasarsa za ta mayar da martani game da wannan kisa a lokaci mafi dacewa.

Shugaban majalisar kolin kasar Iran Ayatollah Ali Khamenei, a ranar Asabar ya bukaci hukumomi da su gaggauta gudanar da bincike kan lamarin tare da hukunta dukkan masu ruwa da tsaki wajen kitsa shi, ya jaddada cewa, kokarin bunkasa kimiyya da fasaha na Fakhrizadeh zai ci gaba da wanzuwa.

Kasar Turkiyya tana adawa da duk wani yunkurin kawo cikas game da shirin wanzar da zaman lafiyar shiyyar, kana tana adawa da dukkan nau’in ta’addanci, ko ma wane ne ke shiryawa kuma ko ma alkan wane ne ake son kaddamarwa kansa, ma’aikatar harkokin wajen kasar Turkiyya ta fitar da sanarwar, inda ta kara da cewa, tilas ne a hukunta dukkan wadanda ke da hannu wajen daukar nauyin harin.

Da take nuna adawa da babbar murya game da kisan, kungiyar tarayyar Turai ta bayyana lamarin a matsayin muggun laifi.

Kasancewar babu wanda ya yi ikirarin daukar nauyin kisan, gwamnatin Iran tana zargin hukumar leken asirin Mossad ta kasar Isra’ila da laifin kaddamar da kisan, kamar yadda kafafen yada labaru suka bada rahoto.

Har zuwa yanzu, Isra’ila bata tabbatar ko kuma musanta zargin da ake yi mata ba. (Ahmad)