logo

HAUSA

Jihar Xinjiang ta dukufa wajen kare tsaro da lafiyar al’ummomi na kabilu daban daban

2020-11-29 16:59:30 CRI

Jihar Xinjiang ta dukufa wajen kare tsaro da lafiyar al’ummomi na kabilu daban daban

A ranar 27 ga wata, gwamnatin jihar Xinjiang ta Uygur mai cin gashin kanta ta kasar Sin ta kira taron manema labarai game da batutuwan dake shafar jihar Xinjiang, inda shugaban kwamitin kiwon lafiya na jihar ya bayyana cewa, ana gudanar da matakan kandagarkin yaduwar cutar numfashi ta COVID-19 a jihar Xinjiang bisa dokokin kasar yadda ya kamata, domin hana yaduwar cutar bai daya a wannan jiha, da kuma kiyaye tsaro da lafiyar al’ummomin jihar na kabilu daban daban kamar yadda ake fata.

Ya ce, bayan barkewar cutar, mutanen da aka tabbatar suna kamuwa da cutar numfashi ta COVID-19 a wannan jiha sun shafi kabilu daban daban. Shi ya sa, bisa jagorancin kwamitin kiwon lafiyar kasar Sin, gwamnatin jihar Xinjiang ta tsaya tsayin daka wajen kebe wurin musamman domin samar da jinya ga masu kamuwa da cutar, da neman dukkanin kwararru likitoci don su samar da jinya yadda ya kamata ga dukkanin masu kamuwa da cutar. Haka kuma, bisa shirin da aka tsara, an ba da jinya ba tare da karbar kudi ba, ga dukkanin masu kamuwa da cutar, da kuma masu kamuwa da cutar wadanda ba su nuna alamun kamuwa da cuta ba.

Sa’an nan, ya kara da cewa, yin kandagarki kan yaduwar cutar numfashi ta COVID-19 yana da muhimmanci matuka wajen kare tsaro da lafiyar al’ummomin jihar, wanda ya kuma kasance babban tushen raya tattalin arziki da zamantakewar al’umma. Jihar Xinjiang tana tsayawa tsayin daka wajen daukar matakan hana yaduwar cutar, yayin da neman bunkasuwar tattalin arziki da zaman al’umma, inda ta tsara manufofi da dama domin samar da guraben aikin yi, inganta harkokin zuba jari, kiyaye yanayin zaman karko ta fuskar harkokin cinikin ketare, da kuma raya masana’antun samar da kayayyaki da sauransu, ta yadda za a rage matsalolin da yaduwar cutar numfashi ta COVID-19 ta haifar wa ci gaban tattalin arziki da zamantakewar al’ummma na jihar Xinjiang.

Cikin farkon watanni 9 na bana, jimillar kimar abin da aka samar a jihar Xinjiang ya kai yuan biliyan 981.994, adadin da ya karu da kashe 2.2 bisa dari idan an kwatanta da na makamancin lokacin bara. A sa’i guda kuma, jihar ta dukufa matuka a fannin kawar da talauci, inda ta samar da manufofi da dama domin farfado da ayyuka a masana’antun taimakawa masu fama da talauci, ta yadda za a tabbatar da samar da ayyukan yi ga masu fama da talauci. Bugu da kari, a ranar 14 ga watan nan da muke ciki, gundumar Yarkant da wasu gundumomi gaba daya guda 10 sun fita daga cikin jerin gundumomi masu fama da talauci, lamarin da ya nuna cewa, dukkanin gundumomin jihar sun fita daga kangin talauci. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)