logo

HAUSA

Sojojin Najeriya sun kashe gomman mayakan Boko Haram a hare hare ta jiragen sama

2020-11-29 15:34:36 CRI

Gomman mayakan Boko Haram ne aka hallaka a wasu jerin hare-hare ta jiragen sama da sojojin Najeriya suka kaddamar a shiyyar arewa maso gabashin kasar, kakakin rundunar sojojin Najeriyar ne ya bayyana hakan.

Sanarwar ta kara da cewa, an kuma lalata wasu daga cikin maboyar mayakan ’yan ta’addan a hare-haren ta jiragen saman da aka kaddamar a ranar Juma’a a kauyen Ngwuri Gana, a kan hanyar garin Gulumba Gana-Kumshe da Tumbuma Baba dake jahar Borno a shiyyar arewa maso gabashin kasar wanda ke makwabtaka da tafkin Chadi.

John Enenche, kakakin rundunar sojojin kasa na Najeriya, ya fadawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa an kaddamar da hare-haren ta jiragen sama ne bayan gudanar da wasu jerin bincike inda aka gano yankunan biyu da mayakan ’yan ta’addan tare da manyan kwamandojinsu ke taruwa domin shirya kaddamar da hare-hare.

Sai dai kuma, jami’in bai bayyana hakikanin yawan ’yan ta’adda da aka kashe ba. (Ahmad)