logo

HAUSA

MDD ta yi kira da a kai zuciya nesa domin kaucewa ta’azzarar yanayi a yankin Gabas ta Tsakiya

2020-11-28 17:03:41 CRI

Sakatare janar na MDD Antonio Guterres ya yi kira da a kai zuciya nesa tare da kaucewa ta’azzarar yanayin yankin Gabas ta Tsakiya, biyo bayan kisan da aka yi wa babban masanin kimiyyar nukiliya na kasar Iran, Mohsen Fakhrizadeh.

A wata wasika da ya aikewa sakatare janar na MDD Antonio Guterres da shugaban kwamitin sulhu na majalisar na watan Nuwamba, Inga Rhonda King, zaunannen wakilin Iran a majalisar, Majid Takht Ravanchi, ya yi kakkausar suka kan kisan.

A cewar ma’aikatar tsaron Iran, wasu ‘yan ta’adda ne suka kashe babban masanin kimiyyar, da akewa lakabi da ‘uban bama baman Iran’, jiya Juma’a a kusa da Tehran, babban birnin kasar.

Kafofin watsa labarai sun ruwaito cewa, gwamnatin Iran na zargin hukumar tattara bayanan sirri ta Isra’ila wato Mossad, da aikata kisan, sai dai Tel Aviv ba ta amsa ko musanta zargin ba. (Fa’iza Mustapha)