logo

HAUSA

Trump ya ce zai fice daga fadar gwamnati muddin kwalejojin zabe suka zabi Biden

2020-11-27 11:06:54 CRI

Trump ya ce zai fice daga fadar gwamnati muddin kwalejojin zabe suka zabi Biden

Shugaban Amurka mai barin gado Donald Trump, ya ce zai fice daga fadar gwamnati ta White House, muddin kwalejojin zabe suka zabi Joe Biden a watan Disamba dake tafe.

Shugaba Trump ya yi wannan tsokacin ne jiya Alhamis, yayin da yake amsa tambayoyin manema labarai, bayan kammala taron ganawa ta kafar bidiyo, da dakarun Amurka masu aiki a kasashen waje, albarkacin bikin cika ciki ko “Thanksgiving”.

Ya ce "Abu ne mai wahala na karbi shan kaye, amma idan har su kwalejojin zabe suka zabi Biden, to sun yi kuskure". Trump ya kuma sake nanata zargin tafka magudi da ya dade yana yi, a babban zaben kasar na ran 3 ga watan nan.

Kafar cibiyar “Cook Political Report” ta ce Joe Biden ya lashe kuri’u 80,218,808, sama da kuri’un 73,947,962 da Trump ya samu. Kaza lika kafofin watsa labaran Amurka sun yi hasashen cewa, Mr. Biden ya samu nasarar lashe kwalejojin zabe 306, fiye da 270 da shugaba Trump ya samu, a zaben na farkon watan nan. (Saminu)