logo

HAUSA

Kabore ya sake lashe babban zaben Burkina Faso

2020-11-27 11:34:54 CRI

Jiya Alhamis, hukumar zaben kasar Burkina Faso, ta gabatar da sakamakon kuri’u da aka kada a babban zaben shugabancin kasar, wanda ya nuna cewa, shugaban kasar na yanzu, Roch Marc Christian Kabore, ya sake lashe babban zaben shugaban kasa.

Bisa kididdigar da hukumar zabe mai zaman kanta a kasar Burkina Faso ta fitar, Mr. Kabore ya samu kuri’u da yawan su ya kai kaso 57.87%, yayin da sauran manyan ‘yan takara guda biyu, suka samu kaso 15.48% da 12.46% na jimillar kuri’un da aka kada.

Daga bisani kuma, kwamitin tsarin mulkin kasar Burkina Faso, zai tantance sakamako da kwamitin harkokin zabe mai zaman kansa ya gabatar masa, sa’an nan, zai sanar da sakamakon babban zaben shugaban kasar a hukumance.

Wa’adin aikin shugaban kasar Burkina Faso shekaru 5 ne, kuma shugaban kasar mai ci na iya sake gudanar da wa’adin aiki sau daya kacal. (Maryam)