logo

HAUSA

UNEP: Afirka na bukatar amfani da dabarun kare muhalli domin gaggauta farfadowa

2020-11-27 11:32:49 CRI

Daraktar shiyyar Afirka ta shirin raya muhalli na MDD ko UNEP a takaice, Juliette Biao Koudenoukpo, ta ce nahiyar Afirka na bukatar rungumar dabarun kare muhalli, domin gaggauta farfadowar sassan ta.

Uwargida Koudenoukpo, ta yi kira ga kasashen nahiyar, da su kara azama wajen ingantawa, da maido da muhalli zuwa yanayinsa na ainihi, su kuma ba da gudummawa wajen gina kyakkyawan yanayi, da fadada ikon yankunansu, na samar da matakan jurewa matsaloli, tare da karkata akalar nahiyar zuwa ga hanyar ci gaba mai dorewa.

Jami’ar ta UNEP wadda ke wannan tsokaci, yayin wani taron masu ruwa da tsaki na nahiyar da ya gudana ta kafar bidiyo, cikin jawabin da wakilinta ya karanta, ta kara da cewa, farfadowa daga kalubalen cutar COVID-19 ya zamewa duniya, musamman ma kasashen nahiyar Afirka, wata muhimmiyar dama ta aiwatar da sauye-sauye.

Ta ce "Cutar COVID-19 ta nunawa duniya irin dunkulewar da duniya ta yi, da kuma yadda sassan duniyar ke da bukatar dogaro da juna ta fuskar tattalin arziki da zamantakewa.

Daga nan sai ta kalubalanci mahalarta taron, game da bukatar wayar da kai, da ilmantarwa, da yayata manufofi, tare da shigar da sassan al’umma, da masu tsara manufofi a dukkanin matakai, cikin ayyukan warware kalubalolin muhalli, da matakan dakile matsalolin da ka iya bijirowa ba zato, don kawo karshen kalubalen da ake fuskanta a yanzu. (Saminu Hassan)