logo

HAUSA

WHO ta bukaci kasashen Afirka da su karfafa shirin su na karbar rigakafin COVID-19

2020-11-27 11:06:38 CRI

Daraktar shiyyar Afirka a hukumar lafiya ta duniya WHO uwargida Matshidiso Moeti, ta yi kira ga kasashen Afirka, da su samar da tsari mai nagarta, da jami’ai masu kwarewa, wadanda za su taimaka wajen karbar rigakafin cutar COVID-19, da zarar an kai ga bukatar hakan.

Matshidiso Moeti, ta ce raba rigakafin ga dukkanin sassa ba tare da wata matsala ba, jigo ne na cimma nasarar dakile cutar, musamman a wannan gaba da ake samun karin bazuwar ta a wasu sassan nahiyar.

Jami’ar wadda ta bayyana hakan cikin wata sanarwa da ofishin ta fitar a birnin Nairobin kasar Kenya, ta kara da cewa, yanzu haka ana daf da fara aiwatar da rigakafi mafi girma a tarihin duniya, don haka ya zama wajibi ga gwamnatocin kasashen Afirka su yi kyakkyawan shiri.

Moeti ta ce "tsara ayyuka, da kasancewa cikin shiri shi ne zai tabbatar da nasara ko akasin ta a wannan aiki, don haka akwai bukatar shugabanci na gari, da kwazo a matakin koli na jagoranci, da cikakken tsarin tafiyar da komai bisa dacewa”.

Sakamakon wani bincike da WHO ta gudanar ya nuna cewa, kasashen Afirka da dama ba sa cikin shirin gudanar da rigakafin cutar ta COVID-19, musamman fannin samar da jami’ai, da tsara gudanar da aikin cikin nasara.   (Saminu)