logo

HAUSA

Yawan mutanen da suka kamu da cutar COVID-19 ya zarce miliyan 60 a duk fadin duniya

2020-11-27 10:39:22 CRI

Hukumar lafiya ta duniya WHO ta gabatar da sabbin alkaluma dake nuna cewa, ya zuwa karfe 6 da mintoci 38 na yamma ranar Alhamis bisa agogon Turai, yawan mutanen da suka harbu da cutar COVID-19 ya kai 60,074,174, kana cutar ta hallaka mutane 1,416,292.

Ban da wannan kuma, kwanan baya, hukumar yaki da cutar ta Amurka America CDC ta ba da rahoton cewa, an yi kiyasin cewa, yawan mamata sakamakon cutar a Amurka kadai, kafin ran 19 ga watan Disamban bana, zai karu zuwa mutum 321,000 daga 294,000.

Bugu da kari, kwamitin kasuwanci da cinikin takardun hada-hadar kudi na Amurka, ya ba da rahoto cewa, cutar ta kara illata lambun shan iska, da gidan shakatawa na kamfanin Walt Disney na Amurka, matakin da ya sa ala tilas ake shirin rage ma’aikatan wurin su 32,000 kafin watan Maris na shekarar badi. (Amina Xu)