logo

HAUSA

Kwararrun wasu kasashe sun nuna amincewa kan fasahohin Sin wajen kawar da talauci

2020-11-26 13:50:50 CRI

Kwanan baya, lardin Guizhou na kasar Sin ya sanar da kawar da dukkanin gundumomi masu fama da talauci daga jerin wurare masu fama da talauci, lamarin da ya nuna cewa, dukkanin gundumomi masu fama da talauci guda 832 na kasar Sin sun fita daga kangin talauci.

Kwararru na wasu kasashen duniya sun nuna yabo matuka kan wannan babbar nasara da kasar Sin ta cimma a fannin yaki da talauci, suna ganin cewa, sauran kasashen duniya suna iya koyon fasahohin kasar Sin a fannin kawar da talauci da raya kasa.

Shugaban sashen nazarin harkokin siyasa ta cibiyar nazarin harkokin gabashin Asiya ta kwalejin kimiyya da fasaha na kasar Rasha, Andrey Vinogradov ya bayyana cewa, kasar Sin ita ce kasa mai tasowa ta farko da ta nuna wa kasashen duniya yadda za a cimma nasarar kawar da talauci, fasahohin Sin ta fuskar yaki da talauci na da muhimmiyar ma’ana ga kasashen duniya.

Mai nazarin harkokin kasa da kasa na kasar Kenya Cavins Adhill ya ce, kasar Sin ta cimma burin neman ci gaba cikin yanayin adalci ta hanyar kawar da talauci a yankunan karkara, wannan shi ne babbar nasara da kasar ta cimma a fannin kawar da talauci.

Ban da haka kuma, kwararru a majalisar ‘yan kasuwa tsakanin Sin da Masar na kasar Masar, da jami’ar Namibia, da Nairobi ta kasar Kenya da sauransu sun cimma ra’ayi daya cewa, kasashe masu tasowa za su iya koyon matakan da kasar Sin ta dauka, da suka hada da inganta harkokin masana’antu, raya kasuwanni cikin gida, da samar da guraben aikin yi ga masu fama da talauci, domin kawar da talauci. Kuma nasarar da kasar Sin ta cimma a wannan aiki ta karfafawa kasashen duniya gwiwa wajen kawar da talauci baki daya. (Maryam)