logo

HAUSA

Labarin yadda Luo Fuhua ‘yar kabilar Li Su take raya sana’a

2020-11-17 20:13:56 CRI

A kauyen Hecun na gundumar Binchuan ta lardin Yunnan, akwai gine-gine biyu masu jawo hankulan mutane sosai, akwai wanda aka gina da itace na musamman, akwai kuma daya ginin mai hawa biyu. Dukkan gine-ginen biyu gida na Luo Fuhua, yar kabilar Li Su, nan ne ta soma sana’arta ta yawon shakatawa a gidan manoma mai salon musamman na kabilar Li Su, inda ta kafa kamfanin saka kyalle na hannu mai suna Huo Caobu. 

A yayin da Luo Fuhua ke magana kan yadda zaman rayuwar iyalinta yake a yanzu, ta ce,

“A lokacin da na fara sana’ar yawon shakatawa a gidajen manoma, babu wanda yake irin wannan sana’a a kauyanmu, iyalina ne suka fara wannan sana’ar a kauyen mu. Kafin mu fara wannan sana’a, babu abin da mu ke yi sai shuka masara da busar da ganyen taba. A lokacin, ina iya samun kudin shiga da ya kai yuan dubu biyu zuwa uku daga masarar da na shuka a ko wace shekara. Kana a bangaren busar da ganyen taba kuwa, nan ma ina iya samun kudin shigan da ya kai Yuan dubu talatin a ko wace shekara. Wadannan su ne ayyuka biyu da na dogaro da su, amma kudin da nake samu ba sa biyan bukatun iyalinmu na yau da kullum.”

Labarin yadda Luo Fuhua ‘yar kabilar Li Su take raya sana’a

Kabilar Li Su dake gundumar Binchuan, tana daya daga cikin kabilu 9 na musamman dake lardin Yunnan, wato yanayin zaman takewar al’ummar kabilun 9 ya samu ci gaba daga zamanin da da can a farkon shekaru 50 na karnin da ya wuce zuwa na zamanin gurguzu kai tsaye. Sakamakon wasu dalilai a fannonin tarihi da halittu da dai sauransu, ‘yan kabilar sun fuskanci koma baya a fannin samar da kayayaki da zaman rayuwa. Amma, a shekarar 2011, an gina wata hanyar mota a kusa da wani tsauni mai na dutsen Ji Zu Shan dake gundumar Binchuan, wannan ya kyautata yanayin sufurin wurin, bayan da aka hada wurare masu ni’ima, da al’adun gargajiya, da kuma raya sana’a yadda ya kamata, inda kuma Luo Fuhua ta samu damar raya sana’arta.

Saboda kauyen Rucun na dab da wuri mai ni’ima na dutsen Ji Zu Shan, don haka Luo Fuhua ta gudanar da sana’ar yawon shakatawa a gidan manoma yadda ya kamata. Masu yawon shakatawa da suka fito daga wurare daban daban na kasar Sin ne suke amfani da gidanta, har ma akwai wadanda suka zo daga kasashen ketare. A wasu lokuta, ta kan ajiye na’urar saka a kofar hotel din ta, idan babu baki da yawa, ta kan saka kyalle. Sakan kyallen hannu wata fasahar gargajiya ce ta wasu ‘yan kananan kabilu mata da dama, ciki har da ‘yan kabilar Li Su mace. Matan kabilar su kan dinka tufaffi ta hanyar sakan kyallen hannu. Ko da yake yanzu an samu kyautatuwar yanayin zaman rayuwa, amma duk da haka wasu iyalan kabilar sun ci gaba da gudanar da wannan fasahar gargajiyar. Kyallen da Luo Fuhua ta saka kyallen gargajiyar kabilar Li Su ne mai suna Huo Cao Bu. Da ma tana daukar sakan kyallen ne a matsayin aikin gida kawai, amma ba ta yi tunanin cewa, tufaffin da aka dinka da kyallen Huo Cao Bu sun jawo hankulan masu yawon shakatawa sosai ba.

“Da farko, ban taba tunanin cewa, abin da nake yi zai jawo hankulan masu yawon shakatawa, sha’awa ce kawai, amma daga baya na gano cewa, akwai wadanda ke son sayen wannan kyallen.”

Sannu a hankali, saka kyallen Huo Cao Bu na kara samun karbuwa. A bisa kokarin da gwamnatin garinsu ta yi, Luo Fuhua ta halarci bikin baje kolin da aka yi a birnin Kunming, hedkwatar lardin Yunnan, inda wani ‘dan kasuwa ya bukaci ta saka masa kyallen na yuan dubu 20, amma kuma ya bukaci a samar da tuffafin a cikin kwanaki 20. Gaskiya ba zai yiwu ba, saboda ita daya ce kawai ta ke aikin, wannan ya sa Luo Fuhua ta hakura da wannan odar.

Labarin yadda Luo Fuhua ‘yar kabilar Li Su take raya sana’a

A shekarar 2017, Luo Fuhua ta kafa wani kamfanin sakan kyallen na Huo Cao Bu, ta dauki iyalai sama da 100 daga kauyuka 4 dake kewayen dutsen Ji Zu Shan, don su raya sana’ar Huo Cao Bu tare. A sakamakon haka, duk iyalin da ya shiga sana’ar yawan kudin shigan da yake samu ya karu zuwa a kalla yuan dubu 15 a ko wace shekara.

Ko da yake sun samu nasara da farko, amma Luo Fuhua ba ta gamsu ba. Ta gargadi yarta wadda ke aiki a birni, da ta komo kauye, ta yi aiki tare da ita. A ganin ta, yar ta na iya kawo sabbin abubuwa a sana’ar. Yarta Hai Huizhen ta ce,

“Yanzu matasa sun fi son yin aiki a birane, ba sa mai da hankali kan al’adun kabilunsu. Ni ma da haka nake, amma daga baya na fahimci cewa, ni ‘yar kabilar Li Su ce, dole ne na koyi saka kyalle da hannu. Yanzu, mazauna kauyenmu suna ba mu goyon bayan ni da mahaifiyata kan yadda za mu raya wannan sana’a.”

A yanzu haka, Luo Fuhua da yar ta suna amfani da yawancin lokacinsu wajen tsara da kuma sanar da tufafin gargajiyar kabilar Li Su. Hai Huizhen tana kuma shirin fara tallata tufaffinsu ta yanar gizo, Hai Huizhen ta ce,

“Ina fatan ni da mahaifiyata ba mu yi zaben tumun dare ba . Yanzu burin mu shi ne kara kawo ci gaban tattalin arziki ga kabilar Li Su dake gundumar Binchuan. Wannan zai sa kowa ya fahimci cewa,ba mu manta da al’adunmu ba, duk da cewa muna zaune a yanki mai tsaunuka.”