logo

HAUSA

Sin ta harba sabon tauraron dan Adama na sadarwa

2020-11-13 10:42:52 CRI

A jiya Alhamis ne kasar Sin ta yi nasarar harba tauraron dan Adama na harkokin sadarwa mai lakabin Tiantong mai lamba 1-02, daga tashar harba kumbuna ta Xichang dake lardin Sichuan, na kudu maso yammacin kasar.

An harba tauraron ne da karfe 12 saura minti 1 na dare bisa agogon birnin Beijing, ta hanyar amfani da rokar “Long March-3B”. Kasar Sin ce ta kera dukkanin sassan tauraron na Tiantong-1. Yana kuma kunshe da sashen na’urar sama jannati, da wanda ake kafawa a doron kasa, da kuma na’urar sarrafa shi.

Rahotanni sun tabbatar da cewa, Tiantong 1-02 zai rika gudanar da hidimar sadarwa ta tafi da gidan ka, da sauran na’urorin da aka kafa a doron kasa, don samar da bayanai masu nasaba da yanayi, kai tsaye, kuma cikin inganci.

Kaza lika zai rika samar da hidimar sadarwa ta sakwannin murya, da gajerun sakwanni, da rubutattun sakwanni a kasar Sin, da ma yankunan kewayen ta, da na gabas ta tsakiya, da Afirka da sauran wasu yankunan masu alaka da su, baya ga mafi yawan yankunan tekun Fasifik da tekun India.

Wannan karo shi ne na 352, da ake amfani da rokar Long March, wajen harba taurarin dan Adam zuwa sararin samaniya.  (Saminu)