logo

HAUSA

Uwa na iya cimma burinta a rayuwa yayin da take kula da 'ya'yanta

2020-11-07 22:10:44 CRI

A kasar Sin, iyaye ba sa watsi da kokarin cimma burikansu, in ma burin na kara ilimi ne ko fara sabon aiki. Wadannan iyaye mata masu yara, sun yi kokarin cimma burikansu kuma sun yi rayuwarsu yadda suke so. Ta hakan, sun kuma haskaka rayuwar 'yayansu. Burin uwa kan yi tasiri a kan rayuwar 'ya'yanta, kuma yana kara nunawa 'ya'yan hanya mafi dacewa tare da bayar da kwarin gwiwa da kuma karfi.

Uwa na iya cimma burinta a rayuwa yayin da take kula da 'ya'yanta

Dai Yingniao, daliba mai karatun digiri na 3 a jami'ar Columbia ta Amurka, ta ce sha'awarta na rubutun adabi ya samo asali ne daga mahaifiyarta, Qin Wenjun, wadda fitacciyar marubuciyar adabin yara ce a kasar Sin. A shekarar 2008, Qin ta zama Basiniya ta farko da aka zaba domin samun lambar yabo ta Astrid Lindgren, wanda ke zaman lambar yabo mafi fice a adabin yara. Dai, ta rubuta littattafai, da sauran nau'ikan adabi, wanda idan aka hada, yawansu ya kai sama da miliyan 1. Saboda tasirin mahaifiyarta, Dai ta fara sha'awar adabi tun tana yarinya. "ina matukar alfahari da aka haife ni cikin iyalin dake kaunar karatu. Da nake karama, na kan ga iyayena suna jin dadin karatu a kowanne dare bayan an ci abinci. Abu mai tsarki ne. A lokacin, ina fatan koyon karatu n ima in bi sahunsu ba da dadewa ba", cewar Dai.

Uwa na iya cimma burinta a rayuwa yayin da take kula da 'ya'yanta

Sauran wasu iyaye ma sun samu damammakin fara sabon aiki yayin da suke kula da 'ya'yansu. Bailu Danfeng da aka haifa a shekarar 1960, daya ce daga cikinsu. Tagwayenta 'yan mata, Chufei da Churan, na aiki ne a matsayin masu gabatar da shirin kai tsaye na wani dandalin cinikayya ta intanet, dake Hangzhou na lardin Zhejiang na gabashin kasar Sin. Su kan sayar da tufafi da kayayyakin kwalliya, kuma suna da mabiya sama da miliyan 1.1. Bayan ta yi ritaya, a shekarar 2016, sai Bailu da mijinta suka koma Hangzhou daga Guangzhou dake lardin Guandong na kudancin kasar Sin domin zama tare da 'ya'yansu. Gabatar da shiri kai tsaye ba aiki ne mai sauki ba. Dole ne masu gabatarwa su ware lokaci mai yawa sannan su kasance cikin kuzari. Domin tabbatar 'yayanta na cin abinci yadda ya kamata, Bailu kan dafa musu abincin rana a kullum, sai mijinta ya kai musu. Chufei da Churan na yawan cin abincin rana yayin da suke gabatar da shiri kai tsaye, kuma galibin masu bibiyarsu kan yi tsokaci kan abincinsu, su kan yi tambaya game da yadda aka girka abincin tare da karfafawa Bailu gwiwar gabatar da shirin kai tsaye kan yadda ake girki. Saboda wannan shawara, Bailu ta fara nata shirin na kai tsaye a shekarar 2017, kuma tun daga lokacin take gabatar da shirinta na girke-girke da yadda take kula da gida. Bailu ta bayyana cewa, "masu bibiyarmu na daukar shirinmu na kai tsaye a matsayin abokin hira…galibin mutane na zaune su kadai ba sa haduwa da iyalansu kullum. Ganin shirinmu kan kwantar musu da hankali". Yanzu Bailu na da mabiya sama da 200,000. Iyayen da suke da burika a zukatansu, sun cimma abubuwan da suke muradi, kuma kwarin gwiwarsu da kaunar da suke wa 'ya'yansu ya karfafawa 'ya'yan gwiwar samun nasara.

Uwa na iya cimma burinta a rayuwa yayin da take kula da 'ya'yanta

Zhou Yasong mai shekaru 56, wadda ta yi wani kwas na neman digiri na biyu a jami'a daya da 'yarta Wu You, ta samu izinin fara karatun digiri na 3 daga jami'ar Jamhuriyar Koriya a ranar 1 ga watan Yuli. Labarin ya yi ta yawo a kafar intanet, inda aka yi ta yabawa Zhou a mastayin mai kokarin cimma burinta. Zhou ta amsa cewa, "buri na ne, kuma sakamakon kokarin da na yi ta yi ne, har yanzu da sauran tafiya a gaba".

Zhou 'yar asalin Changde na lardin Hunan dake yankin tsakiyar kasar Sin, ta yi aiki a matsayin mai tattarawa da adana bayanai a wani ofishin gwamnatin karamar hukuma. 'Yarta ta bude mata wani dakin wake-wake a shekarar 2013, domin koyar da dabarun waka da fiyano ga yara. Shekaru biyu bayan nan, Wu ta fara shirin rubuta jarrabawar yin karatun neman digiri na biyu, kuma ta tsara burin da take son cimmawa, wato karatu a sashen nazarin wake-wake na Jami'ar ilmantar da malamai ta birnin Wuhan na lardin Hubei, dake tsakiyar kasar Sin. Domin rage ayyukan dake gaban 'yarta, Zhou kan raka Wu lokacin da take koyon waka da yin jarrabawa da daukar darasi. Daga bisani, ita ma ta yanke shawarar daukar jarabawar. Rubuta jarrabawar ba buri ne na rana guda ba a wajen Zhou. Bayan kammala makarantar sakandare, Zhou ta samu gurbin karatu a wata kwalejin nazarin fasaha, amma dole ta hakura saboda iyayenta ba za su iya daukar nauyinta ba. Kakan Zhou masanin wakokin gargajiya ne, wanda ke iya amfani da kayayyakin waka da kida da dama, kuma ya yi tasiri a kan Zhou. Saboda tasirinsa, Zhou ta girma tana kaunar wake-wake, kuma ta koyi yin waka da rawa da buga fiyano da wasu kayayyakin kida. Cikin shekaru sama da 30, Zhou ta yi ta koyon dabarun waka da motsa jiki a lokacin da ba ta da wani aikin da za ta yi. Duk da cewa ta haura shekaru 50, tana iya yin wasu atisayen. Ta kammala karatun digiri ta hanyar wani shirin "koyo da kanka" da wata jami'a ta gabatar. A lokacin da take gab da ritaya, ta yanke shawarar kara gwada cimma burinta na kammala koyon waka a wata fitacciyar makaranta. "Ban damu da digiri ba…amma ina kaunar sake zama daliba", cewar Zhou. Ta ce tana son 'yarta ta san cewa mata na iya kokarin cimma burikansu ta hanyar dagewa. Wasu mutane sun bayyana shakku game da kudurin Zhou. "mabanbanta mutane na da ra'ayi mabanbanta. Ina son koyon abubuwa. Koyon abubuwa tsawon rayuwata ne kadai zai gamsar da ni" cewar Zhou. Wu ma ta amince da hakan. Ta yi ta karfafawa mahaifiyarta gwiwa. Wu ta shaidawa mahaifiyarta cewa, " ki yi abun da kike so, kuma ki yi abun da ya dace da zai saki farin ciki." Bayan yanke shawara, Zhou ta gaggauta yin ritaya sannan ta shirya tafiya tare da 'yarta don rubuta jarrabawar. Zhou da Wu, sun kama hayar gida a kusa da Jami'ar ilmantar da malamai ta tsakiyar kasar Sin, kuma tare suke daukar darasin shiryawa jarrabawar.

Uwa na iya cimma burinta a rayuwa yayin da take kula da 'ya'yanta

A watan Afrilun 2016, Zhou ta shiga jami'a, sai dai ba a dauki 'yarta ba. "har yanzu da kuruciyarki. Kina da sauran dama," cewar Zhou, domin karfafawa Wu gwiwa, wadda a kullum ke ganin mahaifiyarta a matsayin tushen kwarin gwiwarta.

A ranar 1 ga watan Satumban 2016, Zhou ta fara rayuwar da ta dade tana buri, wato goya jaka domin shiga aji da cin abinci a dakin sayar da abinci na makaranta da kwanciya a kan gadon dakin kwanan dalibai da karatu a dakin karatu. Zhou na yawaita furuta kalaman da za su sanyaya zuciyar 'yarta, kuma ta kan fada mata yadda rayuwarta ke kasancewa yayin rubuta jarrabawa. Shekara daya bayan nan, Wu ta samu gurbin karatu a jami'ar. Duk da cewa suna zama a dakin kwanan dalibai daya, karatu ba ya bari su rika haduwa akai-akai. Wani lokacin su kan ci abinci tare a dakin cin abinci, kuma idan suna tare, su kan shafe lokacin suna hira da dariya. Zhou ita ce mafi girma kuma mafi kwazo a ajinsu. Ta kan tashi da misalin 6 na safiya a kowacce rana don buga fiyano. Wu na taimaka mata da darrusa masu wahala. "a gaskiya, ina daukar lokaci fiye da matasa kafin in koyi abu. Amma da zuciya mai karfi da lafiya, zan iya tafiya tare da su", cewar Zhou. Yanzu an dauki Wu aiki a wata kwaleji a lardin Hunan. Tana koyar da dabarun rera waka. Idan tana magana kan mahaifiyarta, tana yawaita amfani da kalmomin "kauna" da "dagewa" . A gare ta, a kullum Zhou na da kyakkyawar fata, da kwarin gwiwa ba tare da gajiyawa ba. "Ina son wake-wake, kuma zan ci gaba da koyo. Zan ci gaba da kasancewa aminiyar 'yata. Ina son shaida mata cewa, muddin za ta jajirce kan cimma burinta, to za ta yi nasara, nan ba da dadewa ba. Abun da ba ya shafi shekaru ba ne," cewar Zhou.

Uwa na iya cimma burinta a rayuwa yayin da take kula da 'ya'yanta

A watan Afrilun 2019, Yuan Mengyuan, mai kula da dakunan kwanan dalibai 'yan kasashen waje a jami'ar Jian Tong ta Shanghai a wancan lokaci, ta cinye jarrabawar karatun neman digiri na biyu ta kasa tare da danta.

Yuan mai shekaru 49 a lokacin, ta samu gurbin karatu a jami'ar Guangxi dake Nanning na yankin Guangxi mai zaman kansa dake kudancin kasar Sin, domin nazartar ilimin koyar da Sinanci ga wadanda ba Sinawa ba. Danta kuma, ya shiga jami'ar Fudan dake Shanghai. Yuan ta fito ne daga lardin Henan na yankin tsakiyar kasar Sin. Ta rubuta jarrabawar shiga kwaleji a shekarar 1991, bayan nan kuma, ta shiga kwalejin ilmantar da malamai ta Xinyang, dake birnin Xinyang na lardin Henan. Ta karfafawa mijinta gwiwar ci gaba da karatu. A shekarar 2005, mijinta ya zaman dalibin digirin digirgir a jami'ar Jiao Tong ta Shanghai. Ya kuma zama malami a jami'ar Shanghai bayan ya kammala karatun. Yuan da danta sun koma Shanghai ne a shekarar 2011. Shekara daya bayan nan kuma, danta ya samu gurbin karatu a makarantar sakandare ta Gezhi, daya daga cikin fitattun makaratu a Shanghai. A lokacin da danta ke karatu, ita ma ta kan karanta littattafai. Wanda ya samar musu da wani yanayin karatu mai dadi a gidan. "da yake firamare, na kan zauna kusa da shi, in yana karatu, in kuma sa shi ya mayar da hankali. Amma, maimakon taimaka masa, yana sa shi fargaba. Don haka, na sauya dabara, sai ni ma nake karatu tare da shi", cewar Yuan. Ta karanci yadda ake tausa da lissafin kudi da kula da uwa da jariri, kuma tana da shaidar karantar wadannan fannoni. Tana shiga wasu shirye-shiryen unguwa sosai idan ba ta da wani aiki. A shekarar 2015, danta ya samu gurbin karatu a jami'ar Shanghai, don haka Yuan ta yanke shawarar ci gaba da karatu tare da shi. "Ina jin dadin koyon karatu. Ina son in samu ci gaba tare da dana, in kuma samar masa da yanayin karatu mai kyau," cewarta. A lokaci guda kuma, ta kan halarci ajujuwan Adabi da Sinanci a jami'ar Shanghai. Yanayin jami'ar ne ya sa ta sha'awar ci gaba da karatu. A shekarar 2016, Yuan ta rubuta jarrabawar manya ta shiga kwaleji, bayan nan ne kuma, ta shiga jami'ar Fudan. Ta karanci harshen Sinanci da Adabi. "Na dauki hotuna da yawa na ajinmu, da kuma harabar jami'an Fudan, na kuma nunawa dana. Yanayin jami'ar ya burge shi, kuma ya shaida min cewa, shi ma yana son yin karatu a irin wannan katafariyar jami'a," cewar Yuan. A shekarar 2018, Yuan ta lura da wata tallar neman mai kula da daliban kasashen waje da aka manna a jami'ar Jiao Tong ta Shanghai. Yuan ta nemi aikin, kuma ta samu. "kafin in fara aiki a nan, na halarci wasu ajujuwan Turanci da Sinanci a jami'ar na tsawon shekaru 3, domin muna zaune ne a kusa da jami'ar," cewar Yuan.

Uwa na iya cimma burinta a rayuwa yayin da take kula da 'ya'yanta

A shekarar 2018, lokacin da danta ya fara shirin rubuta jarrabawar karatun neman samun digiri na biyu, ita ma Yuan ta yanke shawarar rubuta jarrabawar. "abun farin ciki ne a gare mu domin muna taimako da karfafawa juna gwiwa", cewarta.

Turanci da ya kasance wajibi, shi ne matsalar Yuan tun tana Firamare, domin ba ta iya ba. Domin kara fahimtar harshen, ta kan kashe lokaci mai yawa tana koyonsa, ciki har da shiga darrusa ta intanet sama da 200. "Babu wani sirri game da koyon Turanci. Kawai na kan maimaita kalmomi akai-akai. A shekaruna, ba na iya tuna abubuwa sosai kamar matasa, amma ba na hakura, ina iya manta kalmomin da na koya da farko, amma ina sake kokarin haddacewa", inji Yuan. Yayin hutun rani a bana, Yuan ta tafi wani kauye mai tsaunuka a yankin Liangshan na kabilar Yi mai cin gashin kansa dake lardin Sichuan na kudu maso yammacin kasar Sin, domin koyar da yara Sinanci da wasu darrusa. "yara a wurin na bukatar kwararrun malamai. Na ji dadi sosai da na ga yaran na kara himmantuwa a aji, kuma sun kara sha'awar koyon karatu," cewarta. Niyyarta shi ne, inganta harkar ilimi a yankunan karkara a kasar Sin. "ina son zama misali ga dana, ina son ya fahimci cewa bai kamata mutum ya yi karatu saboda samun dukiya ko daukaka ba, sai dai domin taimakawa al'umma," cewar Yuan. Kamar sunanta, Mengyuan, wanda ke nufin cimma buri, Yuan ta kan dage wajen karatu domin cimma burikanta. "ina son koyon abubuwa. Na kan mayar da hankalina ga karatu. Idan mutum ya dage, rayuwa za ta zo masa da abubuwan ban mamaki da bai yi zato ba", cewar Yuan.

Ta kara da cewa, "duk wahalar dake akwai wajen neman cimma buri, a karshe burin zai tabbata".(Kande Gao)