logo

HAUSA

Ga yadda matan kasar Sin suke zage damtse wajen fattakar talauci

2020-10-14 09:48:59 CRI

A shirinmu na yau, Fa'iza Muhammad Mustapha ta ci gaba da yi mana bayani game da sauran ziyarce-ziyarcen da ta yi da nufin fahimtar yadda mata a kasar Sin suka zage damtse wajen fattakar talauci. A zangon karshe na tafiyar, ta ziyarci larduna uku da suka hada da Guizhou da Sichuan da kuma Gansu.

A lardin Guizhou, ta ga yadda mata 'yan kabilar Miao suka dukufa wajen raya al'adarsu ta garjiya, wato zane da rini, a hannu guda kuma, suka mayar da shi sana'arsu ta samun abun dogaro da kai.

Matan na amfani da kakin zuma ne wajen kawata yadukan tufafi ko na sauran wasu abubuwa kamar jakunkuna, mayafai da sauransu, sannan sai a rina wadannan yaduka zuwa launuka daban-daban. A baya, wadannan mata kan yi zanen ne a matsayin sha'awa, amma ba don samun kudin shiga ba, amma yanzu bisa taimakon kamfanin wata mata mai suna Malama Ning, sun samu hanyar samun kudin shiga, inda ta dauke su aiki tana biyansu albashi, su kuma suna mata zane da rini. Kuma wannan sabuwar hanya, ta kara wayar musu da kai.

A lardin Sichaun ma matan ne ke kokarin kawar da talauci karkashin jagorancin kungiyar mata. A nan ma dai, an samowa mata da aka sakewa matsuguni hanyoyin kudin shiga, inda ake basu horo a fannoni daban- daban kamar na saka da girke girke. A kokarin gwamnatin Sin na sanya al'ummarta cikin wadata, ta dauke wasu al'ummomi daga mazauninsu na da, wanda bai dace da rayuwa ba a wannan zamani, zuwa sabon matsuguni. Don haka aikin kungiyar matan na da nasaba da kula da matan da aka sakewa matsuguni domin ganin sun fita daga kangin talauci da kyautata rayuwarsu. Haka zalika, kungiyar na sa ido wajen sauya wasu tsoffin dabi'u marasa kyau na 'yan kabilar Dongxiang, kamar na rashin tsafta, inda ta ke ba su kwarin gwiwa ta hanyar sayar musu da kayayyaki amma ba da kudi ba, wato ta hanyar ba su maki bisa yanayin tsaftarsu, inda za su yi amfani da wannan maki wajen sayen kayayyaki a kasuwar da ta kafa.

A lardin Gansu kuma, ta ga yadda mata manya da matasa ke kokarin yaki da dabi'ar kulle da ake musu don ganin sun tsaya da kafarsu. Ta kuma samu damar bin wata matashiya da ta samu ilimin zamani, wadda ta kafa kamfani da nufin samun kudin shiga da kuma taimakawa mata 'yan uwanta don su dogora da kafarsu da wayar musu da kai domin kawar da tsohuwar dabi'ar kulle.

Sana'arsu suma ta al'ada ce, wato saka da allura da zare.

A dukkan wadannan wurare, ta ga yadda mata ke raya al'adunsu da kuma samun kudin shiga a lokaci guda, inda kuma tuni suka yi adabo da talauci. (Faeza Mustapha, Ibrahim Yaya, Sanusi Chen)