logo

HAUSA

Abdulmalik Hamza Bichi: Ina da burin canja tsarin da ake amfani da shi a Najeriya zuwa na zamani

2020-10-13 18:59:54 CRI

Abdulmalik Hamza Bichi: Ina da burin canja tsarin da ake amfani da shi a Najeriya zuwa na zamani

Abdulmalik Hamza, wani dan asaslin garin Bichi ne daga jihar Kanon tarayyar Najeriya, wanda a yanzu haka yake karatun digiri na biyu a jami'ar koyon ilimin noma ta lardin Gansu a birnin Lanzhou dake arewa maso yammacin kasar Sin, bayan da ya gama karatunsa na digiri na farko a jami'ar BUK.

Abdulmalik Hamza Bichi: Ina da burin canja tsarin da ake amfani da shi a Najeriya zuwa na zamani

A zantawarsa da Murtala Zhang, dalibin ya kwatanta ci gaban ayyukan noma gami da yanayin karatu a gida Najeriya da kasar Sin, har ma ya ce kasar Sin ta samu bunkasuwa sosai a fannin ilimi da aikin gona da sauransu, kuma kasa ce da ta cancanci a yi koyi da ita.

Har wa yau malam Abdulmalik Hamza Bichi ya jaddada burinsa na son canja tsarin da ake amfani da shi a gida Najeriya, ya dawo da na zamani, wanda duniya take amfani da shi yanzu, ciki har da kasar Sin.(Murtala Zhang)