logo

HAUSA

Ga yadda nakasassu mata biyu Liu Chunxiang da Li Yaomei suke kokarin kawar da talauci

2020-09-16 08:39:07 CRI

Yayin da kasar Sin ke kokarin fatattakar talauci a karshen wannan shekara da muke ciki, wakiliyarmu Fa'iza Muhammad Mustapha, ta ziyarci wasu yankunan kasar, inda ta ga yadda wasu mata suka dukufa wajen yaki da talauci bisa kokarinsu da kuma tallafin da gwamnatin kasar ta ba su.

Ga yadda nakasassu mata biyu Liu Chunxiang da Li Yaomei suke kokarin kawar da talauci

Da farko, ta ziyarci birnin Yushu na lardin Jilin dake arewa maso gabashin kasar Sin, idan ta ga yadda mata suke amfani da fasaha wajen sarrafa bawon Masara. Wadannan mata da suke samun horo da tallafi daga gwamnati, sun kafa wata kungiya ko kamfani domin halasta sana'arsu, inda suke amfani da bawon masara wajen samar da nau'ika daban daban na kayayyaki. Daga cikin abubuwan da suke samarwa, akwai Jakunkuna, takalma, mafici, fai-fai, malafa da tarin wasu abubuwa da dama.

Baya ga haka, wadannan mata kan yi amfani da fasahar sadarwa ta zamani wajen tallata hajojinsu. Wannan sana'a ta taimakawa mata da dama a yankin wajen dogaro da kansu da samun kudin shigar da ya kyautata musu rayuwa.

Ga yadda nakasassu mata biyu Liu Chunxiang da Li Yaomei suke kokarin kawar da talauci

Baya ga garin Yushu, ta kuma ziyarci kauyen Lonyuan na yankin Hongsipu na birnin Wuzhong na jihar Ningxia ta kabilar Hui, mai cin gashin kanta ta arewa maso yammacin kasar Sin. A nan kuma, ta tarar da wata macen da ke amfani da basirarta wajen raya sana'arta ta kiwo da samar da nau'ikan daban-daban na tsinya, baya ga kirkiro wasu na'urori da za su taimaka wajen saukaka sana'o'inta. Labarin Li Yaomei ya kasance mai taba zuciya, kasancewar ta fuskanci wahalhalu da kalubale da dama a rayuwa, amma wannan bai sa ta yi kasa a gwiwa ba, inda ta dukufa kai da fata wajen yakar talauci. Li Yaomei ta kasance daya daga cikin mutanen da gwamnatin kasar Sin ta dauke daga yankunan da ba su dace da rayuwa ba, inda ta tsugunar da su a wani sabon kauye. Zuwa yanzu, bisa namijin kokari da basirarta, ta kammala biyan bashin yuan 300,000 kwatankwacin naira miliyan 17 da ta taba ci a baya, sannan ta dakatar da karbar tallafi daga gwamnati, kana ta kafa masana'antar samar da tsintsiya tare da daukar ma'aikata. (Sanusi Chen)