logo

HAUSA

Shamsuddeen Garba: Zan yi amfani da ilimin da na koya a kasar Sin don taimakawa kasa ta Najeriya

2020-08-25 15:09:46 CRI

Shamsuddeen Garba: Zan yi amfani da ilimin da na koya a kasar Sin don taimakawa kasa ta Najeriya

Shamsuddeen Muhammed Mukhtar Garba, wani dan jihar Kanon tarayyar Najeriya ne wanda a yanzu haka yake karatun digiri na farko a fannin hada manhajoji na na'ura mai kwakwalwa a jami'ar kimiyya da fasahar kere-kere dake birnin Changchun na kasar Sin, wato Changchun university of science and technology a turance. A zantawarsa da Murtala Zhang, malam Shamsu ya bayyana dalilin da ya sa ya kudiri aniyar karatu a kasar Sin, musamman ganin yadda kasar ta samu babban ci gaba a fannoni daban-daban. Shamsu ya kuma ce, irin karamci da abutar da al'ummar Sinawa suka nuna masa ya burge shi kwarai da gaske. Da ma an ce zo ka ci tuwo, aka ce ya fi tuwon dadi.

Malam Shamsuddeen Muhammed Mukhtar Garba ya kara da cewa, da zarar ya kammala karatu a kasar Sin, burinsa shi ne ya koma gida Najeriya domin taimaka mata samun ci gaba.(Murtala Zhang)