logo

HAUSA

Aminu Hussaini Adamu Gumel: Noma tushen arziki

2020-07-28 14:33:03 CRI

Aminu Hussaini Adamu Gumel: Noma tushen arziki

Aminu Hussaini Adamu Gumel, wanda aka fi sani da suna Aminu 1 Naira, wani dalibin Najeriya ne wanda a yanzu haka yake karatun digiri na biyu a jami'ar koyon aikin gona ta kasar Sin dake Beijing.

Aminu Hussaini Adamu Gumel: Noma tushen arziki

A zantawarsa da Murtala Zhang, Aminu 1 Naira ya bayyana cewa, ko da yake bai jima da zama a kasar ta Sin ba, amma ya ganema idanunsa babban ci gaban da kasar ta samu a fannoni daban-daban, har ma ya ziyarci wuraren yawon shakatawa da na tarihi da dama a kasar, inda ya ji dadin yadda mutanen kasar Sin ke kulla zumunci da baki 'yan kasashen waje, musamman bakake fata.

Aminu Hussaini Adamu Gumel: Noma tushen arziki

Aminu 1 Naira, wanda a yanzu haka yake gudanar da ayyukan gwaji a fannin aikin gona a karkashin jagorancin malaman jami'arsa a lardin Hebei na kasar Sin, ya ce kasar Sin ta samu babban ci gaba wajen gudanar da aikin gona, ganin yadda take da fasahohi gami da na'urorin zamani masu tarin yawa. Aminu ya kuma bayyana fatansa ga matasan Najeriya don su bada muhimmanci kan ayyukan gona, saboda a cewar malam Bahaushe, noma tushen arziki.(Murtala Zhang)