logo

HAUSA

Bundesliga na duba yiwuwar daukar 'yan kwallo daga Sin

2020-07-16 20:06:41 CRI

Mashirya gasar kwallon kafa ajin kwararru ta kasar Jamus ko Bundesliga, na sanya ido kan kungiyoyin kwallon kafar Sin, da niyyar daukar 'yan wasa daga kasar, domin bugawa kulaflikan dake buga gasar ta Bundesliga a nan gaba. A cewar jagoran Bundesliga Robert Klein, manyan kungiyoyin kwallon kafar Jamus, na fatan samun karin karbuwa sama da sauran takwarorin su na Turai a kasar Sin, inda suke kuma fatan kara fadada kasuwar su a kasar mafi yawan al'umma a duniya. Robert Klein ya ce "Muna fatan samun karin dan wasa daya daga Sin, ko 'yan wasa biyu, ko uku cikin Bundesliga. Mai yiwuwa hakan ya faru cikin sauri, muna fatan nan da kakar wasanni mai zuwa mu cimma nasarar hakan". Jami'in ya ce ana dora muhimmanci kan kasuwar Sin, inda kawo yanzu, cikin kungiyoyi 18 dake buga Bundesliga, 6 na da ofisoshin su a Sin. Kaza lika ana gudanar da musaya tsakanin Sin da Jamus a fannin tamaula, musamman a bangaren horas da 'yan wasa. Mr. Klein ya kuma yi waiwaye game da tarihin shekaru 20 na gasar Bundesliga da ke kara samun karbuwa a kasar ta Sin. Ya ce "Binciken mu ya nuna cewa, muna da tarin magoya baya a Sin, kuma muhimmin abu a nan shi ne, kara samun kusanci da magoya baya musamman a wannan lokaci na cin gajiyar fasahohin zamani. Klein ya ce Bundesliga, ta kara fadada bayanai da harkokin ta a kafofin sada zumunta daban daban dake kasar Sin, domin kara biyan bukatun Sinawa. Karkashin wannan manufa, kungiyoyin dake buga Bundesliga na yada harkokin su ta shafukan da suka hada da Weibo, da WeChat, da Douyin ko Tik-Tok. Mr. Klein ya kara da cewa, "Muna daukar matakan kusanto da magoya bayan mu dake Sin, ta yadda za su samu damar cudanya da kungiyoyin mu, da ma 'yan wasan kwallon kafar mu," "Muna fatan tattaunawa da magoya bayan mu Sinawa ta hanyar da za ta iya yin tasiri gare su." A baya bayan nan an gabatar da shirin musamman mai taken "Der Klassiker" wanda ya yi sharhi game da karawar Bayern Munich da Borussia Dortmund, da kuma karawar Dortmund da kungiyar Schalke 04.

An kuma kaddamar da wata manhajar ba da hidimar kididdiga ta wasannin gasar Bundesliga. Manhajar wadda kamfanin Amazon ya samar, tana baiwa magoya bayan kungiyoyin kwallon kafa damar yin mahawara game da yiwuwar jefa kwallo a zare yayin da ake taka leda, ko tattaunawa game da yanayin kwallon da aka riga aka zura a raga.