logo

HAUSA

Liverpool za ta lashe Premier a karon farko tun bayan shekara 30

2020-06-12 15:54:35 CRI

Liverpool za ta ci gaba da sa kaimi na lashe kofin Premier bana, inda za ta kara da Everton ranar 21 ga watan Yuni da zarar an ci gaba da gasar 2019-20 ba 'yan kallo. Wannan ne karon farko da Liverpool za ta ci kofin Premier League tun bayan shekara 30. Shin a wane wasan ne za ta dauki kofin bana? Ranar 17 ga watan Yuni za a ci gaba da wasannin Premier League na shekarar nan da kwantan wasa tsakanin Aston Villa da Sheffield United da na Manchester City da Arsenal. Cikin watan Maris aka dakatar da wasannin tamaula a Ingila sakamakon bullar cutar korona, daga baya kungiyoyin da ke buga gasar Premier suka amince za su karkare kakar 2019-20. Liverpool tana ta daya a kan teburin Premier da tazarar maki 25 tsakaninta da Manchester City, kuma wasa biyu za ta ci a ba ta kofin bana a karon farko tun bayan shekara 30. Sai dai kuma Liverpool din za ta iya cin kofin da zarar Arsenal ta doke Manchester City ita kuma kungiyar ta Anfield ta yi nasara a kan Everton. Wasu kwanakin da ake ganin za a bai wa Liverpool kofin Premier na shekarar nan sun hada da ranar 24 ga watan Yuni lokacin da za ta karbi bakuncin Crystal Palace ko kuma 2 ga watan Yuli a wasa da Manchester City. Dan wasan Liverpool Mohamed Salah ya ci kwallo 16 a kakar bana yana kan-kan-kan da Sergio Aguero na Manchester City a mataki na uku a jerin wadanda ke kan gaba a cin kwallaye a Premier bana. Dan kwallon Leicester City, Jamie Vardy shi ne kan gaba da kwallo 19 a raga sai kuma dan wasa Arsenal, Pierre-Emerick Aubameyang mai 17 a raga. Ranar ta 19 ga watan Yuni Tottenham wadda take da takwas a teburin Premier za ta karbi bakuncin Manchester United, ita kuwa Leicester City wadda take ta uku za ta ziyarci Watford ranar 20 ga watan Yuni. A dai ranar ta Asabar da za a ci gaba da wasanni Arsenal za ta je Brighton and Hove Albion, yayin da Aston Villa za ta kece raini da Chelsea ta hudu a teburi ranar 20 ga watan Yuni. Manchester City za ta kara wasa ranar Litinin 21 ga watan nan, inda za ta yi wa Burnley masauki. Za a nuna wasannin da za a ci gaba da gasar Premier League a talabijin wadda za a fafata ba 'yan kallo don gudun yada cutar korona. Timo Werner: Chelsea ta ƙulla yarjejeniyar ɗauko ɗan wasan RB Leipzig Chelsea ta kulla yarjejeniya domin dauko dan wasan RB Leipzig Timo Werner. Rahotanni sun ce za a sayar da dan wasan mai shekara 24, wanda ya ci kwallo 25 a gasar Bundesliga a kakar wasan da muke ciki, a kan £54m. Ana ta rade radin cewa dan wasan dan kasar Jamus zai koma Liverpool ya kuma ce yana alfahari da jin dadin alakanta shi da batun. Amma an fahimci cewa Liverpool ba ta sha'awar sayen Werner, wanda ya ci wa tawagar Jamus kwallo 11 a wasa 29 da ya yi. Chelsea na shirin daukar Timo Werner Liverpool ba ta da niyyar sayo dan wasa ko daya idan aka bude kasuwar musayar 'yan kwallo. Olivier Giroud ne kadai mai ci wa Chelsea kwallo da ke da lafiya, bayan da Tammy Abraham ke jinya tun cikin watan Janairu. A watan jiya ne dan kwallon tawagar Faransa, Giroud ya sanya hannu kan yarjejeniyar ci gaba da zama a Chelsea zuwa kakar wasa daya. Werner zai kasance dan wasa na biyu da Chelsea za ta saya don buga wasa a kaka mai zuwa bayan kammala sayen dan wasan Ajax Hakim Ziyech a watan Fabrairu a kan £37m. Ya burge Leipzig bayan komawa kungiyar a shekarar 2016 daga Stuttgart. Werner ya ci kwallo uku a wasan da Leipzig ta doke Mainz da ci 5-0. A watan Janairun an alakanta kocin Chelsea, Frank Lampard da cewar zai sayo dan wasan Paris St-Germain, Edinson Cavani da kuma na Napoli, Dries Mertens, ko da yake hakan zai yiwu ba. Real Madrid ta bayar da euro 80m don sayo Havertz, Everton za ta ɗauko Rabiot Real Madrid ta mika euro 80m domin sayo dan wasan Bayer Leverkusen Kai Havertz kuma za ta kyale dan wasan na Jamus mai shekara 20 ya ci gaba da zama a kungiyarsa ta yanzu zuwa kakar wasa ta baɗi kafin ya koma Bernabeu. Chelsea za ta yi maraba da kungiyoyin da ke son daukar 'yan wasanta da dama bayan isar dan wasan Morocco Hakim Ziyech, mai shekara 27, daga Ajax da kuma dan wasan Jamus Timo Werner, mai shekara 24, dagaRB Leipzig a bazarar nan. Shugaban Red Bull Leipzig Oliver Mintzlaff ya musanta cewa Chelsea ta cika sharudan biyan £53m a kan Werner, yana mai cewa babu kungiyar da ta "aiko mana da kwangilar musayar 'yan kwallo". KocinLiverpool Jurgen Klopp ya bayyana Havertz da Werner a matsayin "manyan" 'yan wasa amma ya ce matsalolin da annobar korona ta kawo za su iya shafar shirinsa na dauko su. Man Utd na son ɗauko Kai Havertz, Leicester 'bata yi ko gezau ba' kan Chilwell Saura nasara biyu a bai wa Munich kofin Bungesliga Everton tana kan gaba a fafutukar dauko dan wasan Juventus da Faransa mai shekara 25 Adrien Rabiot, wanda a 2012 kocin Everton Carlo Ancelotti ya soma sanya shi a wasa a tsohuwar kungiyarsa Paris St-Germain. Chelsea tana fuskantar kalubale daga kungiyoyi akalla bakwai a yunkurin da take yi na dauko dan wasan Ingila Ben Chilwell daga Leicester, wadda ake matsawa lamba domin ta sayar da dan wasan mai shekara 23. Arsenal da Wolves suna sha'awar dauko dan wasan Italiya mai shekara 25 Daniele Rugani, wanda ya yi ta fama wajen ganin an sanya shi a tawagar farko a Juventus lokacin jagorancin Maurizio Sarri. Manajan Netherlands Ronald Koeman ya ki amsa tayin komawa Barcelona a watan Janairu saboda ba ya so ya ci amanar tawagar kasar Netherlands. Suarez zai buga wa Barcelona wasa bayan kwana 147 yana jinya Luis Suarez ya murmure zai kuma ci gaba da buga wa Barcelona sauran wasannin La Liga da suka rage a bana, bayan kwana 147 da likitoci suka yi masa aiki. Ana kuma sa ran dan kwallon zai buga wa Barcelona wasan da za ta fafata da Real Marca ranar 13 ga watan yuni da za a ci gaba da wasannin 2019-20. Ranar 12 ga watan Janairu aka yi wa likitoci suka yi wa Suarez aiki, inda suka gindaya masa karshen kakar bana zai murmure. Wasan karshe da ya buga wa Barcelona shi ne karawa da Atletico Madrid a farkon makon Janairu a wasan daf da karshe a Spanish Super Cup. Suarez ya koma atisaye a cikin watan Mayu, bayan wata hudu rabonsa da taka leda, kawo yanzu ya koma kan ganiyarsa zai iya buga wa Barca sauran wasannin La Liga da suka rage a bana. Dan wasan na tawagar Uruguay ya ci kwallo 14 a wasa 23 da ya buga wa Barcelona a kakar shekarar nan, guda 11 a La Liga da uku da ya ci a Champions League. Duk da jinya da Suarez ya yi shi ne ke mataki na uku a jerin wadanda suka bayar da kwallo aka zura a raga a gasar ta La Liga, inda yake da takwas. Tun cikin watan Maris aka dakatar da wasannin La Liga don gudun yada cutar korona, bayan da Barcelona ce ta daya a kan teburi da tazarar maki biyu tsakaninta da Real Madrid. An ya za a iya kammala gasar Serie A ta bana kuwa? Cikin watan nan za a ci gaba da gasar Serie A don karkare kakar 2019-20, bayan da aka dakatar da wasanni a cikin watan Maris don gudun yada cutar korona. Ranar 20 ga watan Yuni ake sa ran ci gaba da gasar bana kuma tuni aka fitar da jadawalin wasannin da suka rage na shekarar nan da za a yi ba 'yan kallo. Sai dai kuma ana ganin da kyar ne idan za a iya kammala gasar ta Serie A saboda dokar killace 'yan wasa idan an samu mai dauke da cutar korona. Mai Brescia ya ce ya yi kuskure da ya dauki Mario Balotelli Coronavirus: Minista ya kira shugabnnin Gasar Serie A 'masu taurin kai' Kamar gasar Jamus ta Bundesliga da ta Premier League an kafa doka cewar da zarar an samu dan kwallo dauke da annobar zai killace kansa, amma kungiyarsa za ta ci gaba da atisaye da wasanninta. Sai dai a Italiya ba haka dokar take ba, bayan da gwamnati ta ce da zarar an samu dan wasa daya dauke da cutar korona to kungiyar gaba daya za ta killace kanta mako biyu. A jadawalin da aka fitar na ci gaba da gasar Serie A kungiyoyi za su buga wasa biyu a mako daya tun daga 20 ga watan Yuni zuwa 2 ga watan Agusta don karkare kakar bana. Sai dai dokar killace kungiya mako biyu za ta kawo tsaiko a ci gaba da gasar ta Italiya domin za a iya shiga rudani da zarar kungiyoyi da dama na hukuncin killace kansu idan an samu 'yan wasansu dauke da annoba.

Cikin watan Maris aka dakatar da dukkan wasannin Serie A don gudun yada cutar korona, bayan da Italiya tana daga cikin kasashen da annobar ta tagayyara a duniya.