in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
• Majalisar NPC za su mai da hankali kan kare muhalli da sauran fannoni masu muhimmanci 2014-03-10
Asabar 9 ga wata, shugaban majalisar wakilan jama'ar kasar Sin NPC, mista Zhang Dejiang, ya yi bayani a gaban wakilan jama'a kimanin dubu 3 dangane da ayyukan zaunannen kwamiti na majalisar, a ci gaban taron shekara-shekara na majalisar NPC, hukuma mai ikon mulki na koli na kasar Sin...
• Sin na da imanin cimma karuwar cinikayyar waje da kashi 7.5 bisa dari  2014-03-07
A ranar 7 ga watan nan ne aka shirya wani taron manema labaru, dangane da tarurrukan nan 2 da ake gudanarwa a nan birnin Beijing, inda ministan kasuwancin Sin Mista Gao Hucheng ya zanta da manema labaru kan batutuwan da suka shafi raya harkokin kasuwanci, da bude kofar kasar Sin ga duniya. Mista Gao ya ce, Sin tana da imanin cimma burin samun karuwar cinikayyar waje da kashi 7.5 bisa dari...
• Za a samar da wata kyakkyawar makoma ta bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin  2014-03-06

An shirya taron manema labaru karo na farko na taron shekara-shekara, na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin wato NPC a ran 5 ga wata, inda daraktan kwamitin raya kasa da yin kwaskwarima na kasar Mista Xu Shaoshi, ya zanta da manema labaru kan bunkasuwar tattalin arziki, da zamantakewar al'umma, da kuma matakan da gwamnati ta dauka kan manyan fannonin. Mista Xu ya ce, a bana an samu wani mafari mai kyau ga bunkasuwar tattalin arzikin Sin, kuma za a samar da wata kyakkyawar makoma ta bunkasuwar. Sin tana da sharadi, da kwarewa, da kuma imani wajen cimm burin samun saurin karuwar tattalin arziki zuwa kashi 7.5 bisa dari...

• Gwamnatin Sin ta tsara shirin ayyukanta na shekarar 2014, a kokarin zurfafa gyare-gyaren da take yi  2014-03-05
Yau Laraba 5 ga wata da safe ne, a nan Beijing, aka bude taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin, wadda ita ce hukumar koli ta kasar. A yayin bikin bude taron, Li Keqiang, firaministan kasar ya gabatar da rahoton ayyukan gwamnati a madadin sabuwar gwamnati, inda ya jaddada muhimmancin yin gyare-gyare a gida a gaba da kome...
• Kasar Sin ta himmatu wajen aiwatar da kwaskwarima a kokarin neman bunkasuwa tare da kasashen duniya 2013-12-30

A shekarar 2013, kasar Sin ta fara aiwatar da kwaskwarima a dukkan fannoni tun bayan da sabuwar gwamnati ta haye karagar mulkin kasar. A lokacin da aka yi cikakken zaman taro karo na 3 na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 18, a watan Nuwamba, an sanar da shirin kasar na zurfafa kwaskwarima a shekaru 10 masu zuwa. Shekarar 2014 ta kasance shekarar da kasar Sin ta soma aiwatar da wannan shirin, To, wane irin tasiri ne kasar Sin za ta kawo wa duniya? Yanzu ga cikekken bayanin.

• Masanan Amurka na sa ran ganin Sin ta kara bude kofa da yin kwaskwarima 2013-11-07

A nan gaba kadan za a kira cikakken zaman taro karo na uku na kwamitin tsakiya na 18 na jam'iyyar kwamins ta Sin, a cewar masu fashin baki a Amurka dake mai da hankali kan harkokin kasar Sin, shugabannin kasar Sin za su gabatar da matakan da za su dauka yayin taron domin gudanar da kwaskwarimar da za ta kawo amfani sosai ga sauyin hanyar da Sin take yi a fannin tattalin arziki da al'umma.

  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China