in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin da MDD za su zurfafa hadin gwiwarsu a fannin samar da hatsi
2019-06-21 13:16:51 cri
Hukumar ajiyar hatsi da sauran kayayyaki ta kasar Sin, da hukumar abinci ta duniya WFP, sun kulla wata yarjejeniyar fahimtar juna a kwanan baya, a birnin Zhengzhou na kasar Sin, inda bangarorin 2 suka tabbatar da niyyarsu, ta zurfafa hadin kai a fannin samar da hatsi, da yada fasahohi masu ci gaba na kasar Sin ga sauran kasashe masu tasowa, ta yadda za a samu damar tabbatar da tsaron abinci a duniya.

Wajen bikin kulla yarjejeniyar, wani jami'in hukumar WFP, Stanlake Samkange, ya ce kasashen duniya za su iya koyon fasahohin kasar Sin, wadda ita ce aminiyar WFP, wajen yin hadin gwiwa, a kokarin kau da yunwa da tsananin talauci a duniya. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China