in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kamfanin Huawei ya kare kansa sakamkon shirinsa na tinkarar hadari a lokacin da ake zaune lafiya
2019-05-19 17:11:17 cri


Duk da yake ba ta da wata cikakkiyar shaida, a ranar 16 ga wata, ma'aikatar kasuwancin kasar Amurka ta sanar da tanadin kamfanin Huawei na kasar Sin da sauran kamfanoni 70 masu alaka da shi cikin takardar jerin sunayen kamfanonin da Amurka ta hana sayar musu kaya. Amurka ta hana kamfanin Huawei ya sayi fasaha ko kayayyakin sauyi daga dukkan kamfanonin Amurka, a yunkurin katse hanyar cinikin kamfanin na Huawei, hana bunkasuwar kasar Sin ta fuskar kimiyya da fasaha ta zamani, da kiyaye yadda Amurka take yin babakere a duniya a fannin kimiyya da fasaha.

Hakika dai abun da ya faru ya wuce zaton Amurka. Kamfanin Huawei ya kaddamar da shirin farfadowa nan take, shirin da ya dauke goman shekaru yana zuba kudi a kai, ta yadda ya tabbatar da ci gaba da sayar da yawancin kayayyakinsa a nan gaba. Kamfanin Huawei ya samu nasarar tsallake yunkurin Amurka na kai mata hari.

A matsayinsa na kamfani mafi girma a duniya na samar da na'urorin Intanet, kamfanin Huawei yana samarwa mutanen da yawansu ya wuce kashi 1 cikin kashi 3 na jimillar mutanen duniya hidimar aikin sadarwa ta yau da kullum, amma ya gamu da cikas da yawa wajen yin cinikayya a Amurka, ya zuwa yanzu, ba zai iya shiga kasuwannin ababen more rayuwar jama'a na aikin sadarwa na Amurka ba.

Koda yake haka ne Amurka ta damu ganin yadda kamfanin Huawei ya zama na farko a duniya wajen samun lambobin kira na fasahar 5G. Kasar Amurka ba ta son kowace kasa daban da ta yi takara da ita a cikin gasar fasahar 5G. Don haka, ta bada kariya wajen yin ciniki da sunan "tabbatar da tsaron kanta", tare da daukar matakai daban daban wajen kai farmaki ga kamfanin Huawei.

A maimakon tabbatar da tsaron kanta da kuma kyautata karfinta, abubuwan da Amurka ta yi sun kawo babbar illa ga kamfanonin Amurka wadanda suka hada kai da kamfanin Huawei, sun sanya 'yan Amurka dubu gomai sun rasa aikin yi, tare da raunana hadin gwiwar kamfanonin kasa da kasa wajen samar da kaya, har ma sun haddasa koma bayan al'adun dan Adam da ci gaban kimiyya da fasaha. Tuni wasu shugabannin kasashen Turai sun ce, ba za su hana kamfanin Huawei kamar yadda Amurka take yi ba. Lamarin da ya nuna cewa, kasashen duniya ba su ji dadin rashin kunyar da Amurka ta yi ba wato kai farmaki ga saura a yunkurin kiyaye matsayinta.

Abin farin ciki shi ne kamfanin Huawei ya tsara shirinsa na farfadowa yau shekaru gomai da suka wuce, ya kuma dauki tsawon lokaci yana share fagen kiyaye kansa a cikin mawuyacin hali.

Haka lamarin yake kasar Sin da ma al'ummar Sinawa. Cikin shekaru 70 bayan kafuwar jamhuriyar jama'ar kasar Sin, wannan kasa na fuskantar matsin lamba daga ketare koda yaushe ba tare da kakkautawa ba. Amma a karkashin shugabancin JKS, jama'ar Sin suna rubanya kokarinsu tare da share fage sosai domin samun wadatuwar kasa da jin dadin zamaninsu. A karshe dai sun canza yanayin fargaba zuwa yanayin lumana, sun kuma canza hadari zuwa zarafin da za su iya yin amfani da shi.

Yanzu haka kasar Sin tana kusan kaiwa ga cimma manufarta ta farfado da al'ummar Sinawa. Amma kamar yadda shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya fada, wannan manufa ba ta da saukin cimmawa. Tabbas ne za a kara yin kokari, za a kuma kara share fagen tinkarar batutuwan ba-zata, da yin rigakafin barazana da kalubale.

Yadda kamfanin Huawei ya samu nasarar murkushe yunkurin Amurka na kai mata hari, ya taimakawa mutanen Sin wajen kara fahimtar muhimmancin tsara shirin tinkarar hadari a lokacin da ake zaune lafiya, da kuma kara inganta aniyarsu na jure wahala, da warware matsala, da yin gwagwarmaya da yin kirkire-kirkire. Muddin kasar Sin ta ci gaba da kimanta yiwuwar shiga mawuyancin hali da kuma share fage sosai, tabbas ne za ta samu nasarar murkushe yunkurin kai mata hari, za ta samu kyakkyawar makoma a karshen al'amari. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China