in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jakadan Congo Brazzaville: al'adun kasa da kasa suna daidai wa daida da juna
2019-05-19 16:23:51 cri
Jakadan jamhuriyar Congo dake kasar Sin, Daniel Owassa, ya yi hira da wakilin CRI a jiya Asabar, inda ya nuna yabo kan ra'ayin kasar Sin na neman samun daidaituwa da cudanya tsakanin al'adu na kasashe daban daban. A cewarsa, wasu al'ummu suna ganin cewa al'adunsu na da matsayin da ya fi na sauran mutane, wato tamkar akwai bambancin matsayi tsakanin al'adu daban daban. Wannan ra'ayi, a cewar jakada Owassa, wani babban kuskure ne. A hakika, dukkan al'adu suna da matsayi ne iri daya, sa'an nan ya kamata al'ummu masu al'adu daban daban su yi hakuri da juna, da neman kara dankon zumuncin dake tsakaninsu. Jakadan ya ce babban taron musayar ra'ayi tsakanin al'adun Asiya da ya gudana a birnin Beijing na kasar Sin kwanakin baya, wani dandali ne da dukkan kasashen duniya za su more shi. Ya ce, yana fatan ganin karin kasashe na sauran nahiyoyi su ma za su samu damar halartar irin wannan taro a nan gaba. (Bello Wang)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China