in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Stephen Roach: Karyar da Amurka ta shararawa Sin
2019-05-17 20:24:28 cri

A kwanakin nan Stephen Roach, babban mai bincike a cibiyar harkokin kasa da kasa ta Jackson ta jami'ar Yale ya rubuta wani sharhi dake cewa, 'yan siyasar Amurka na wannan lokaci sun amince da wasu kalaman karya kan kasar Sin, inda suka zargi kasar ta Sin da duk wata matsala da Amurka ta shiga.

A ranar 26 ga watan Afrilun wannan shekara ce, wani shafin intanet ya wallafa wani sharhi mai taken "Bayanan karya da Amurka ta rubuta a kan kasar Sin". Sharhin ya bayyana cewa, abin mamaki, yanzu jam'iyyun Republican da Democrats na Amurka wadanda a baya ba sa zama a inuwa guda, yanzu ra'ayinsu ya zo daya kan wani muhimmin batu: Zargin kasar Sin kan duk halin da Amurka ta shiga. Sai dai bangaren kasar Sin bai taba cewa komai ba.

Sai dai, ya ce, yadda wadannan sassa ke zargin kasar Sin, a matsayin barazana ga mafarkin kasar Amurka, ya haifar da mummunan sakamako. Yanzu dukkan sassan biyu sun sanyawa juna haraji, an samu tsanantar bazaranar tsaro, gargadi game da sabon yakin cacar-baka, da kuma fargabar fito na fito na soja tsakanin manyan kasashen. Yanzu haka kuma duniya na kokarin dunkulewa

Sharhin ya ce, a bangaren cinikayya, a shekarar 2018, kasar Amurka ta samu gibin cinikayyar hajoji da kasar Sin da ya kai dala biliyan 419, amma abin da Trump da galibin sauran 'yan siyasar kasar ba za su yarda ba shi ne, Amurka ta samu gibin cinikayya da kasashe 102 a shekarar 2018. Wannan ya nuna koma bayan kudaden ajiyar cikin gidan kasar, abin da ya haifar da wagegen gibin kasafin kudi da majalisar dokokin kasar gami da shugaban kasar suka amince. Sannan ba a amince da yadda aka gurgunta hanyoyin samar da kayayyakin kasar ba, sakamakon gudummawar da ka bayar a wasu kasashen, amma aka kera aka kuma shigo da su daga kasar Sin, ana ganin hakan shi ne ya fara haifar da rashin daidaiton cinikayya tsakanin Sin da Amirka da ya kai kimanin kaso 35-40 cikin 100. Kuma tattalin arzikin cikin gida da sabbin matakan da ba sa samar da kayayyakin na duniya sun amfani masu sayayya na Amurka. Haka kuma, yana da sauki a dora laifi kan kasar Sin a matsayin kadangaren bakin tulo ga sake bunkasuwar Amurka.

Abu na gaba shi ne, idan aka yi la'akari da batun satar 'yancin mallakar fasaha. Yanzu an yarda cewa, a ko wace shekara kasar Sin tana satar 'yancin mallakar fasahar Amurka na daruruwan biliyoyin daloli, matakin da ke dakushe karfin kirkire-kirkiren Amurka. Sharhin ya dogara da wannan ikirari ne kan wata majiya dake cewa, a shekarar 2017, hukumar dake cewa, tana kare 'yancin mallakar fasaha, 'yancin mallakar fasaha da aka sata ya sa tattalin arzikin Amurka hasarar dala biliyan 225 zuwa 600.

Baya ga wannan kiyasi, irin wadannan alkaluma, an same su ne ta hanyoyi marasa tabbas, wadanda ke kokarin kimanta bayanan sirri na cinikayya da aka sata ta ayyukan da ba su dace ba, kamar safarar miyagun kwayoyi, cin hanci da rashawa, zambar ayyuka, safarar kudade ta barauniyar hanya.

Kasar Sin ta samu bayanan zargin sata ne daga hukumar kwastan ta Amurka da bayanan sintirin kan iyakoki, wadanda suka ba da rahoton cewa, an kwace kayayyaki marasa inganci da na jebu da suka kai dala biliyan 1.35 a shekarar 2015. Haka kuma ita Amurka ta bayyana samun irin wadannan bayanai na kaso 87 cikin 100 na kasar Sin.

Sharhin ya bayyana cewa, baki daya, Amurka ba ta da wasu gamsassun bayanai, ko alkaluma, ko shaidu, kuma Amurkawa ba su yarda da wannan bayanin ba. Maganar ita ce, kar su karyata rawar da kasar Sin take takawa wajen rura tankiyar tattalin arzki da Amurka, amma su jaddada bukatar nuna gaskiya da adalci wajen zargin mai laifi, musamman ganin yadda har yanzu akwai sauran rina a kaba a takaddamar da ake ciki, abin bakin ciki, fakewa da wani abu shi ya fi sauki maimakon mutum ya kalli kansa a madubi.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China