in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta kafa tsarin samar da wutar lantarki da karfin kwal mai tsabta mafi girma a duniya
2019-05-17 15:24:36 cri
Shugaban hukumar makamashin kasar Sin Zhang Jianhua ya yi jawabi a wurin dandalin tattauna kimiyyar zamani kan ayyukan samar da wutar lantarki mai tsabta na kasa da kasa na shekarar 2019, inda ya nuna cewa, Sin ta riga ta kafa tsarin samar da wutar lantarki da karfin kwal mai tsabta mafi girma a duniya, kuma sashen takaita fitar da hayaki mai gurbata muhalli na tashar samar da lantarki mai amfani da kwal ya dara kilowatt miliyan 800, wanda yake sahun gaba a duniya.

An ce, a matsayin kasa da ta samar da kuma kashe makamashi mafi yawa a duniya, yawan tsabtaccen wutar lantarki da Sin ta samar na sahun gaba a duniya, kuma Sin ta kan kyautata tsari dangane da shi. Yawan na'urorin samar da wutar lantarki dake amfani da makamashin da ba ya bukatar mai ko kwal da Sin ta samar ya kai kashi 40 bisa dari, yayin da wutar lantarki da suka samar ya kai kashi 30 bisa dari. (Amina Xu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China