A jiya Alhamis ne dai kamfanin na Huawei ya kaddamar da wayar salula kirar Mate 20 X (5G), wanda ita ce sabuwar kirar wayar kamfanin ta baya bayan nan mai dauke da fasahar 5G. Wayar za ta baiwa masu amfani da ita damar amfani da yanar gizo mai matukar sauri, da batiri mai rike caji, da babbar fuska, tare da sauran hidimomi masu ban sha'awa. (Saminu)