in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta nuna damuwa game da halin da ake ciki a Sudan
2019-05-17 10:59:43 cri
Kakakin babban magatakardar MDD Stephane Dujarric, ya bayyana damuwar majalissar game da yanayin da ake ciki a kasar Sudan, musamman game da sabani tsakanin majalissar soji ta rikon kwaryar kasar da kuma jagororin masu zanga zanga.

Stephane Dujarric, ya ce abu mafi dacewa shi ne dukkanin masu ruwa da tsaki su dora muhimmnaci kan warware sabani, su kuma tabbatar da daukar matakan da za su dakile duk wani yanayi na tashin hankali, da tabbatar da tsaron lafiyar fararen hula, tare da tabbatar da daidaito a daukacin sassan kasar. Jami'in ya kara da cewa, yana da muhimmanci a kare hakkin al'umma na gudanar da zanga zanga cikin lumana.

A jiya Alhamis ne dai shugaban majalissar sojin dake rikon kwarya a Sudan ko TMC Abdel-Fattah Al-Burhan, ya bayyana dage ci gaba da tattaunawa tsakanin masu ruwa da tsaki a siyasar kasar har na tsawon kwanaki 3, bayan da jami'an tsaro suka yi dauki ba dadi da masu zanga zanga a birnin Khartoum, ya kuma bayyana wasu sharudda na sake komawa teburin shawarwari.

Kafin hakan a ranar Laraba, TMC da wakilan kungiyoyin "Freedom" da "Change Alliance", sun amince da damka ikon kasar hannun majalisun kasar uku, kana sun amince da wa'adin shekaru 3 kafin mika mulki ga zababbiyar gwamnati, inda ake fatan tabbatar da zaman lafiya a daukacin sassan kasar cikin watanni 6 na farkon wa'adin. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China