in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tinkarar abubuwan rashin tabbas da kalubalen da duniya ke fuskanta na bukatar hadin gwiwar dukkan kasashe
2019-05-17 10:54:24 cri
Sabon zaunannen wakilin kasar Sin a ofishin MDD dake Geneva, Chen Xu, ya ce rashin tabbas da duniya ke ciki da kalubalen da dan Adam ke fuskanta, na bukatar dukkan kasashe su hada hannu don aiki tare.

Chen Xu ya bayyana haka ne a jiya, yayin da yake mika takardar aikinsa na sabon wakilin kasar Sin ga Darakta Janar na ofishin MDD a Geneva, Micheal Moller.

Da yake bayyana Geneva a matsayin daya daga cikin cibiyoyin huldar diflomasiyya ta kasa da kasa mai muhimmanci, Chen Xu ya ce martaba huldar kasa da kasa buri ne na yawancin kasashen duniya, kuma a shirye tawagar kasar Sin a Geneva take, ta yi aiki da ofishin wajen inganta dangantaka da karfafa hadin kan kasa da kasa tare da bada gudunmuwa ga gina al'umma mai kyakkyawar makoma.

A nasa bangaren, Micheal Moller, ya bayyana amincewarsa da sabon wakilin na kasar Sin, yana mai cewa, duniyar yanzu na bukatar huldar kasa da kasa, kuma muhimmancin Geneva a matsayin cibiyar huldar diflomasiyya tsakanin kasashe na karuwa.

Ya kuma shaidawa Chen Xu cewa, MDD na bada muhimmanci ga matsayin kasar Sin, kuma ta na yabawa irin gudunmuwar da take bayarwa ga karfafa tsarin huldar kasa da kasa. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China