in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MOC: Sin na adawa da daukar wasu matakai bisa manufar tsaro maras adalci
2019-05-17 10:20:27 cri
Kakakin ma'aikatar cinikayyar kasar Sin Gao Feng, ya ce kasar sa na adawa da daukar wasu matakai bisa manufar tsaro maras adalci kan kamfanonin ta, kuma za ta kare hakkin kamfanonin a duk inda suka gudanar da harkokin su.

Gao ya bayyana hakan ne a jiya Alhamis, biyowa bayan sanarwar ma'aikatar harkokin cinikayyar Amurka, wadda ta sanya kamfanin Huawei da abokan huldar sa, cikin jerin kamfanonin da sashen lura da masana'antu da tsaron kasar Amurka suka yiwa shingen ma'amala da kamfanonin ta a fannin hana saya ko musayar fasahohi da kamfanonin Amurka.

Jami'in na Sin ya ce har kullum, kasar sa na umartar kamfanonin ta da su kiyaye dokokin wuraren da suke hada hada cikin su, da dokokin hada hadar fitar da hajoji, su kuma kare dokokin kasashen da suke hulda da su.

Daga nan sai Gao ya yi kira ga Amurka, da ta dakatar da aiwatar da manufofi marasa dacewa, ta rungumi matakan gudanar da kasuwanci da hadin gwiwa tsakanin kamfanonin kasashen biyu, domin kaucewa kara tsanantar yanayin kawancen tattalin arziki da na cinikayya tsakanin kasashen biyu. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China