in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Masu ra'ayi daya da Steve Bannon makiyan Amurka ne
2019-05-16 20:39:24 cri

A 'yan kwanakin nan, Steve Bannon tsohon babban mashawarcin shugaban kasar Amurka, mutumin da ya saba yin maganganun banza ya sake bayyana don duniya ta ji shi. Tun bayan da aka kori shi daga mukaminsa, ba abin da yake kullum sai kokarin shafa wa kasar Sin kashin kaji, domin neman sake dawo martabarsa. A halin yanzu, wato yayin da gwamnatin Amurka ta sake kara wa kayayyakin kasar Sin harajin kwastam, Bannon yana ganin cewa, lallai wannan wata kyakkyawar dama ce gare shi, don haka ya rubuta wani dogon bayani, inda ya zargi kasar Sin a matsayin babbar makiyiyar Amurka, har ma ya tunzura tsohon mai gidansa da kada ta yi rangwame a "yakin tattalin arziki" da Sin, sai dai ya ci gaba da kara sanyawa kayayyakin kasar Sin harajin.

Zargi mafi muni da Steve Bannon ya yi shi ne makarkashiyar da yake kulluwa na bata sunan kasar Sin cewa, kasar Sin tana son nuna fin karfi a duniya, hakan ya nuna cewa, Steve Bannon ya dade yana da tunanin fin karfi a zuciyarsa. Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya sha jaddadawa a fili cewa, duk da cewa kasarsa tana samun ci gaba cikin sauri, amma ba zai yiyu ba ta nuna fin karfi har abada, haka kuma ba zai yiyu ba ta yiwa sauran kasashen duniya mulkin mallaka, saboda ba ta son jefa sauran kasashen cikin wahalhahun da ita kanta ta taba sha. Hakika zai yi wahala da 'yan siyasar Amurka masu son kai wadanda suke aiwatar da manufar mai da hankali kan moriyar Amurka kawai su fahimci irin wannan manufa ta bautawa jama'a.

Koda a jiya Laraba 15 ga wata, wasu 'yan majalisar dattijai na kasar Amurka sun sanar da mika wani daftarin doka ga majalisar dokokin kasar, inda suka bukaci a daina baiwa jami'an Sinawa dake aiki a hukumomin nazarin aikin soja da wadanda suka taba karbar gudummawa daga wannan hukuma takardar visa ta Amurka, don rage hadarin tsaron kasar Amurka. A wannan rana, fadar shugaban kasar Amurka wato White House ta sanar da sanya dokar-ta-baci, da hana kamfanonin kasar Amurka amfani da na'urorin sadarwa da za su kawo illa ga tsaron kasar. Bangarori daban daban na ganin cewa, Amurka ta dauki wannan mataki ne domin kamfanin Huawei.

A yayin da ake raya tattalin arzikin duniya na bai daya a yanzu, kasar Amurka wadda ta kasance kasa mafi ci gaba a fannonin kimiyya da fasaha, da aikin soja, da tattalin arziki a duniya tana kaffa-kaffa da harkokin tsaron kasar, har ta fara rufe kofofinta ga kasashen duniya, wannan abin mamaki ne. A hakika, kasar Amurka ce za ta rushe kanta da kanta. A halin yanzu, 'yan Amurka masu ra'ayin rikau da ke goyon bayan yin takara ba tare da hadin kai da nuna fin karfi a siyasance su ne abokan gaban kasar.(Masu Fassara: Kande, Jamila, Zainab, ma'aikatan sashen Hausa na CRI)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China