in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dole a nuna sahihanci yayin da Sin da Amurka ke tattaunawa kan tattalin arziki da cinikayya
2019-05-16 19:52:11 cri

Jiya Laraba sakataren kudin Amurka Steven Mnuchin ya bayyana cewa, kasar Sin da Amurka sun gudanar da tattaunawa mai yakini kan tattalin arziki da cinikayya tsakanin manyan jami'an kasashen karo na 11, shi da wakilin cinikayya na kasar Robert Lighthizer suna fatan sassa biyu za su ci gaba da gudanar da tattaunawar da suke yi a birnin Beijing. kan wannan, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Lu Kang ya jaddada cewa, muddin ana bukatar samun ci gaba mai ma'ana, dole ne a nuna sahihanci.

Lu Kang ya bayyana yayin taron ganawa da manema labaran da aka saba yi a birnin Beijing cewa, irin matakan da Amurka ta dauka yayin tattaunawar da suka yi, dole ne a sake jaddada cewa, ya zama wajibi a nace ga ka'idojin da aka tsara, wato dole ne a martabar juna da samun moriyar juna, kana dole ne a cika alkawarin da aka dauka, bai kamata ba a karya alkawarin da aka dauka kamar yadda ake so.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China