in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ba za ta shiga wata tattaunawar kasashe uku kan rage makaman nukuliya ba
2019-05-16 19:46:51 cri

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin, Lu Kang ya bayyana cewa, kasarsa ba za ta shiga wata tattaunawar kasashe uku game da yarjejeniyar rage makaman nukiliya ba, ta kuma nanata manufar kare kanta ta fuskar soja.

Lu Kang ya bayyana hakan ne a taron manema labarai da aka saba gudanarwa, yayin da yake amsa tambayar da aka yi masa game da kalaman baya-bayan nan da karamin sakartare a ma'aikatar harkokin wajen kasar Amurka Andrea Thompson ya yi game da sanya kasar Sin cikin tattaunawar Amurka da Rasha kan yarjejeniyar da za ta hana sassan uku kera makaman nulkiya.

Jami'in na kasar Sin ya bayyana cewa, kudaden da kasar Sin take kashewa a bangaren tsaronta ba masu daga hankali ba ne. Kana har kullum tana inganta karfinta na nulkiya ne domin tsaron kasa, wanda ko kusa bai kai na kasashen Amurka da Rasha ba.

Don haka, kakakin ya bukaci Amurka da ta sauke nauyin dake wuyanta bisa hakki da gaskiya ta rage yawan makamanta na nukiliya, ta kuma kulla yarjejeniyar takaita makamai da kasar Rasha.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China