in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin: Duk matakin da Sin ke dauka ya zama martani ne da take mayarwa Amurka
2019-05-16 11:08:16 cri

Kasashen duniya na nuna damuwa sosai ga kara bugawa juna haraji da Sin da Amurka suke yi a sabon zagaye, a kan hakan, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang, ya bayyana a ranar 15 ga wata cewa, duk matakin da Sin take dauka yanzu, don mayar da martani ne ga matakin da Amurka ta dauka ba gaira ba dalili, da nufin kiyaye moriyarta wanda ta dace da doka, da kuma kiyaye manufar dake tsakanin bangarori daban-daban da tsarin ciniki cikin 'yanci.

Hakazalika, Geng Shuang ya ce, Amurka ta yi kirarin cewa, masu sayayya na Amurka ba za su dandana kudar matakin da gwamnati ke dauka ba, ya sabawa hakikanin halin da ake ciki, Sin ta yi kira ga Amurka da ta gyara tunaninta don fahimtar hakikianin halin da take ciki da komawa hanyar da ta dace, ta yadda za ta iya bin hanya iri daya da kasar Sin take bi. (Amina Xu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China