in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Masanan ketare sun yaba wa jawabin Xi Jinping a yayin bikin bude taron tattaunawa game da wayewar kan Asiya
2019-05-16 10:42:23 cri

Jiya Laraba ne aka bude taron tattaunawa game da wayewar kan Asiya a nan Beijing, inda shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya ba da jawabi mai taken "zurfafa yin mu'amala da koyi da juna ta fuskar al'adu, a kokarin raya al'umma mai kyakkyawar makoma ga 'yan Asiya".

Masana da kwararru na kasashen waje suna ganin cewa, jawabin Xi Jinping ya yi karin bayani kan muhimmanci tattaunawa tsakanin mabambantan al'adu cikin adalci, zai kuma kara azama kan yin mu'amala da koyi da juna tsakanin al'adu daban daban.

Hassan Ragab, shugaban kwalejin Confusious na jami'ar Suez Canal ta kasar Masar ya ce, shugaba Xi Jinping ya gabatar da shawarwarinsa filla-filla, wadanda za a iya aiwatar da su yadda ya kamata, lamarin da ya sake nuna sahihancin kasar Sin, na kara azama kan bunkasuwar tattalin arzikin Asiya da yin mu'amalar al'adu, da kuma kyautata zumuncin da ke tsakanin jama'ar nahiyar. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China