A ranar Litinin ne dai majalissar dake lura da harkokin kasashen waje a kungiyar ta EU ta fitar da wata sanarwa, inda ta bayyana damuwa game da tasirin matakan soji da ake dauka a birnin Tirabulus, tana mai cewa matakan soji ba za su iya warware rikicin kasar ba. Kaza lika majalissar ta bukaci sassan biyu da su koma teburin shawarwarin da MDD ke marawa baya.
Gwamnatin Libiyan ta yi na'am da wannan kira, tana mai shan alwashin kawo karshen zaman doya da man ja, tare da fatan kasashen dake taimakawa sojoji tsagin yan adawa za su daina yin hakan, kasancewar matakan sun sabawa kudurorin kwamitin tsaro na MDD.
Har ila yau, majalissar ta yi kira ga kasashen dake da ruwa da tsaki a batun kasar, da su yi nazari kan matakan da suke dauka, wadanda suka sabawa dokokin kasa da kasa, musamman masu nasaba da burin da ake da shi na wanzar da tsaro da zaman lafiya, da daidaito a kasar ta Libiya, da ma yankin da take ciki baki daya. (Saminu Alhassan)